Rashin tsaro: Fiye da Katsinawa 2,226 sun yi hijira zuwa Gombe

Rashin tsaro: Fiye da Katsinawa 2,226 sun yi hijira zuwa Gombe

Shugaban sansanin 'yan gudun hijira na jihar Gombe, Abba Jatau, ya ce fiye da mutane 2,226 ne suka yi hijira zuwa sansanin 'yan gudun hijira da ke Gombe.

Jatau ya bayyana hakan ne a cikin jawabin da ya gabatar yayin da wakilan majalisar dinkin duniya suka kai ziyara sansanin 'yan gudun hijira da ke Wuro Shie a jihar Gombe.

Ya bayyana cewa, ya zuwa ranar Litinin, akwai mutane 38,793 da ke zaune a sansanin 'yan gudun hijira da ke jihar Gombe.

A cewarsa, mazauna sansanin 'yan gudun suna shan wahala saboda karancin abubuwan more rayuwa.

"Jama'a sun zo mana daga jihar Katsina sakamakon rashin tsaro da suke fama da shi a can, yanzu akwai mutane 41,019 a sansanin 'yan gudun hijira.

"Mu na fuskantar kalubale ta fuskar daukar nauyin mutanen da ke zaune a sansanin 'yan gudun hijira.

"Tashin hankali da halin rashin tsaro da ake fama dasu a can, sune silar dawowarsu nan," a cewar Jatau.

A nasa jawabin, jagoran tawagar majalisar dinkin duniya, Edward Kallon, ya ce kimanin mutane miliyan 10.6 ne ke zaune a sansanin 'yan gudun hijira sakamakon rigingimu a sassan duniya daban-daban.

A wani labarin da ya shafi batun rashin tsaro, wasu 'yan bindiga da ake zargin cewa 'yan fashi ne sun kai hari ofisoshin rundunar 'yan sanda a Egbu da ke Owerri da kuma Nkworji da ke yankin karamar hukumar Nkwerre a jihar Imo.

Rashin tsaro: Fiye da Katsinawa 2,226 sun yi hijira zuwa Gombe
Rashin tsaro: Fiye da Katsinawa 2,226 sun yi hijira zuwa Gombe
Asali: Twitter

'Yan bindigar da suka kai hari ofishin 'yan sanda na Nkwerre ranar Litinin, sun yanki wani dan sanda da wuka sannan sun kwace bindigarsa.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun cinnawa motar 'yan sanda wuta kafin su bar ofishin 'yan sandan.

KARANTA: Yadda muka kashe gagararren dan ta'adda, Terwase Gana - Rundunar soji

KARANTA: Yahoo-yahoo: An kama 'yan Najeriya hudu da laifin damfarar Banki a kasar waje

Wata majiya ta bayyana cewa dan sandan da aka garzaya da shi zuwa asibiti sakamakon raunin da ya samu ya mutu ranar Talata.

Majiyar ta bayyana cewa; "wasu 'yan ta'adda da ake zargin 'yan fashi ne sun kaiwa 'yan sanda hari a Owerre Nkworji.

"Sun cinnawa motar 'yan sanda wuta sannan sun raunata dan sanda guda ta hanyar caccaka masa wuka.

"An garzaya da sho zuwa asibitin garin Orlu a ranar Litinim din amma kuma ya mutu ranar Talata," a cewar majiyar.

Kazalika, wasu 'yan bindigar sun kai wani harin daban a ofishin 'yan sanda na Egbu da ke Owerri, babban birnin jihar Imo.

Wani shaidar gani da ido ya ce 'yan bindigar da suka kai hari ofishin 'yan sandan sun kwace bindigar dan sanda daya bayan sun raunta shi ta hanyar caccaka ma sa wuka a wani salo irin na 'yan bindigar farko.

Yayin da aka tuntubeshi, kwamishinan 'yan sandan jihar Imo, Isaac Akinmoyed, ya tabbatar da cewa an kaiwa mutanensa hari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel