Lauyan da yayi murnar mutuwar Kyari da Funtua, da fatan mutuwar Buhari ya rasu
Wasu 'yan Najeriya sun yi rubutu a kafar sada zumuntar zamani na Facebook, tare da tunawa da wani lauyan Najeriya bayan mutuwarsa.
Kamar yadda suka bayyana tare da tuna wallafe-wallafensa, sun nuna yadda ya dinga murnar mutuwar wasu, shafin Linda Ikeji ya wallafa.
Ya yi wallafar murnar mutuwar shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Marigayi Abba Kyari da kuma makusancin shugaba Buhari, Isa Funtua.
Wani abokin marigayin lauyan, ya tabbatar da rasuwarsa bayan wallafar da ya yi a shafinsa na Facebook.
A cikin kalaman turanci ya rera baituka masu ratsa zuuciya a kan abokin nasa mai suna Nnanna Ehiribe.
Ya yi masa fatan samun rahamar Ubangiji a yayin da ya amsa kiran mahaliccinsa.
Babu bata lokaci kuwa ma'abota amfani da kafar sada zumuntar zamanin ta Facebook, suka dinga tururuwa wurin bayyana wallafe-wallafensa na murnar mutuwar wasu.
Ga wasu daga cikin abubuwan da jama'a suka wallafa a kansa:
KU KARANTA: Boko Haram: Ma'aikacin jinya ya kubuta bayan kwashe wata 8 a hannun 'yan ta'adda

Asali: Facebook

Asali: Facebook
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng