Rundunar 'yan sanda ta sa kyautar N500K ga wanda ya tona mabuyar kwararren makashi Shodipe

Rundunar 'yan sanda ta sa kyautar N500K ga wanda ya tona mabuyar kwararren makashi Shodipe

Rundunar ‘yan sandan jihar Oyo ta sanar da saka kyautar N500,000 ga duk wanda ke da gamsasshen bayani abin dogaro da zai yi sanadiyar sake kama Sunday Shodipe, wani madugun mai kashe mutane.

Shodipe mai shekaru 19, ya kasance babban wanda ake zargi a kashe-kashe daban-daban da aka yi a yankin Akinyele na Ibadan.

‘Yan sanda sun kama mai laifin a watan Yuli sannan aka adana shi a ofishin ‘yan sandan Mokola, amma sai ya tsere daga inda aka tsare shi a ranar 11 ga watan Agusta.

Tserewar Shodipe ya haddasa cece-kuce da zanga-zanga a kan rashin kwarewar rundunar ‘yan sandan da ya tsare a karkashin kulawarsu.

Rundunar 'yan sanda ta sa kyautar N500K ga wanda ya tona mabuyar kwararren makashi Shodipe
Rundunar 'yan sanda ta sa kyautar N500K ga wanda ya tona mabuyar kwararren makashi Shodipe Hoto: The Cable
Asali: UGC

Nwachukwu Enwonwu, kwamishinan ‘yan sandan jihar, ya daura laifin tserewarsa a kan wani jami’in dan sanda da ke hutun aiki.

A cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, Fadeyi Olugbenga, kakakin ‘yan sandan jihar, ya ce Enwonwu ya sanar da bayar da kyautar N500,000 ga duk wanda ke da bayani da zai taimaka wajen sake kama mai laifin.

Ya ce duk wanda ya san maboyar mai laifin ya sanar da ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko kuma ya tuntubi rundunar ta layukan da aka amince da su, jaridar The Cable ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Ayo Salami: Ibrahim Magu ya na so ya san jerin zargin da ke kan wuyansa

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Oyo, CP Joe Nwachukwu Enwonwu, psc na fatan bayyana kyauta mai tsoka na dubu dari biyar (N500,000) ga duk wanda ya bayar da bayanai masu amfani da zai kai ga kama wanda ake zargin a karamar hukumar Akinyele na jihar Oyo, wani mai suna Sunday Shodipe dan shekara 19, wanda aka kama tare da gurfanar dashi a hedkwatar rundunar ‘yan sandan Oyo a ranar 17 ga wayan Yuli, 2020. Amma daga bisani sai ya tsere daga hannun hukuma a ranar 11 ga watan Agusta 2020,” in ji sanarwar.

Saboda haka ana bukatar hadin kan jama’a domin kama shi da kuma mika shi ga ofishin ‘yan sanda mai kusa. Ana iya tuntubar rundunar ta lambobin waya kamar haka: 08035632410 da 07066003536.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel