'Yan majalisar jam'iyyar PDP sun yi barazanar tsige Buhari saboda matsalar tsaro

'Yan majalisar jam'iyyar PDP sun yi barazanar tsige Buhari saboda matsalar tsaro

'Yan jam'iyyar PDP, na Majalisar Wakilai ta tarayya sun ce za su fara shirin tsige Shugaba Muhammadu Buhari muddin ba a dena sharrin da ake nufin yi wa Majalisar Tarayya ba da kuma daukan mataki kan rashin tsaro a kasar.

'Yan majalisar na PDP sun sanar da hakan ne a ranar Litinin ta bakin shugabansu, Kingsley Chinda inda ya ce sun bawa bangaren zartarwa waadin sati hudu "su samar da tsaro a Najeriya kana su dauki mataki kan rashawar da ke faruwa a NDDC da EFCC."

Sun ce idan ba haka ba, "Za mu yi amfani da sashin kudin tsarin mulki da suka dace domin fara shirin tsige shugaban kasa domin cigaban Najeriya da yan Najeriya," kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

'Yan majalisar PDP sun yi barazanar tsige Buhari saboda matsalar tsaro
'Yan majalisar PDP sun yi barazanar tsige Buhari saboda matsalar tsaro. Hoto daga Daily Trust.
Asali: UGC

Kafin a tsige shugaban kasa, ana bukatar amincewar kashi biyu cikin uku na majalisun wakilai na tarayya da dattijai. Dukkan majalisun biyu suna da yan majalisa 469.

DUBA WANNAN: Wani ya kashe kansa a harabar ofishin hukuma saboda tarar N215,000

Shafin Intanet na Majalisar Tarayyar ya nuna cewa PDP ba ta da rinjaye a majalisun tarayyar biyu, jimillar yan majalisun PDP 174 yayin da jimillar yan majalisun APC kuma 247.

Duk da hakan yan majalisar na Jamiyyar PDP sun ce za su fara shirin tsige shugaban kasar saboda irin rashin mutuntunsu da bangaren zartarwa ke yi tare da rashin biyaya ga kundin tsarin mulki.

"Idan za a iya tuna wasu abubuwa uku da suka faru cikin makonnin da suka shude. A ranar Alhamis 16 a watan Yulin 2020, Sakataren dindindin na Ma'aikatar Kwadago ya tashi ya fice yayin da kwamitin harkokin yan Najeriya mazauna kasashen waje ke ganawa da shi," inji sanarwar.

"Karamin Ministan Kwadago, Festus Keyamo shima ya tashi ya yi tafiyarsa ana cikin tsakiyar ganawa da shi da kwamitin majalisar ta kwadago da daukan ayyuka saboda rashin jituwa da suka samu kan amsar wasu tambayoyi.

"Kwanaki kadan da suka shude, Mukadashin shugaban Hukumar Cigaban Niger Delta, Daniel Pondei, shima ya tashi ya fice yayin da ya ke ganawa da kwamitin majalisar wakilai ta bincike a kan zargin bannatar da kudade a hukumar."

'Yan majalisar na PDP sun ce duk da cewa bangarorin gwamnatin uku tare suke aiki, babu wanda ya fi wani muhimmanci.

'Yan majlisar jam'iyyar adawar sun kuma yi ikirarin cewa bangaren zartarwa ta mayar da bangaren sharia da majalisar tamkar ba su da wani muhimmanci.

Kazalika, sun kuma koka a kan kisar kiyashin da ake yi wa yan Najeriya a sassa daban daban.

Sun koka kan yadda Boko Haram da yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke cin karensu babu babbaka yayin da gwamnati ta gaza magance matsalolin.

"Ba zai yiwu a matsayin mu na 'yan PDP ba mu koma gefe muyi shiru kamar babu abinda ke faruwa a lokacin da ake lalata demokradiyya tare da rashin girmama kudin tsarin mulki. Ya zama dole bangaren zartarwa ta dena raina Majalisa," a cewar sanarwar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel