Bayan watsa musu kasa a ido, shugabannin majalisar dokoki sun ziyarci Buhari

Bayan watsa musu kasa a ido, shugabannin majalisar dokoki sun ziyarci Buhari

Bayan rikice-rikice da ya auku tsakanin mutanen da Buhari ya nada da mambobin majalisar dokokin tarayya, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, da Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, sun ziyarci Buhari.

Buhari ya karbi bakuncinsu ne da yammacin Alhamis, 16 ga watan Yuli, 2020.

Hadimin Buhari kan shafukan yanar gizo, Bashir Ahmad ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita.

Yace: "Shugaba Buhari ya karbi bakuncin shugaban majalisar dattawa, Dr Ahmad Lawan da Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbaja, da ranan nan a fadar shugaban kasa dake Abuja"

A ranar Talata, majalisar dattawa ta shiga ganawar sirri na gaggawa kan hukuncin ma’aikatar kwadago na ci gaba da shirin daukar ma’aikata 774,000.

‘Yan majalisar dokokin tarayyar sun zargi Keyamo da kwace shirin daukar ma’aikatan daga hukumar daukar ma’aikata ta kasa, wacce ta samu naira biliyan 52 domin aiwatar da shirin.

Sai dai, Keyamo ya fada wa manema labarai a ranar Talata, cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bukace shi da ya ci gaba da shirin daukar ma’aikatan ba tare da la’akari da matsayar majalisar dokoki ba a kan lamarin.

Hakan bai yiwa yan majalisar dadi ba saboda bayan sabanin da suka samu da karamin minista Festus Keyamo, sun bada umurnin dakatar da shirin gaba daya.

Amma yanzu Buhari ya ce Keyamo ya cigaba da harkar gabansa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng.

Asali: Legit.ng

Online view pixel