Dole sai an yi sulhun da ‘ya ‘yan jam’iyya kafin a iya zaben shugabanni inji Audu Soja

Dole sai an yi sulhun da ‘ya ‘yan jam’iyya kafin a iya zaben shugabanni inji Audu Soja

- Abdulazeez Yar’Adua ya bukaci a sasanta rigimar da ke tsakanin ‘Ya ‘yan APC

- Kanal Abdulazeez Musa Yar’Adua ya ce dole ayi sulhu kafin a iya shirya zabe

- ‘Dan siyasar na Katsina ya ba shugabannin rikon kwaryan APC su dinke baraka

Kanal Abdulazeez Musa Yar’Adua, wanda ya na cikin manyan kusoshin jam’iyyar APC a jihar Katsina, ya yi magana game da kalubalen da APC ta ke fuskanta a halin yanzu.

Shugaban kungiyar ‘yan takarar APC, Abdulazeez Musa Yar’Adua, ya yi kira ga shugabannin rikon kwarya da aka nada da su yi kokarin dinke barakar da ke dankare cikin jam’iyya.

Mutawallen Katsinan ‘Danuwa ne wurin tsohon shugaban kasa Marigayi Ummaru Musa Yar’adua. Kanal Abdul’aziz Musa Yar’adua ya bi layi, inda ya ke da burin takarar gwamna ko sanata a Katsina.

‘Dan siyasar ya nemi sababbin shugabannin wucin-gadin su shawo kan duk wasu matsalolin cikin gidan APC, wanda a cewarsa an kyakyanshe kwan sabanin ne tun a 2018.

Abdulazeez Musa Yar’Adua ya ce rigimar APC ta samo asali ne tun daga zaben tsaida ‘yan takara da aka yi a 2018, inda aka fuskanci wasu matsaloli da jam’iyyar ta gaza shawo kan su har abin ya yi kamari.

KU KARANTA: 'Ya 'yan El-Rufai sun yi wa 'Dan Atiku taron rubdudu a Twitter

Dole sai an yi sulhun da ‘ya ‘yan jam’iyya kafin a iya zaben shugannni inji Audu Soja
Abdulazeez Musa Yar’Adua
Asali: Facebook

“”Ya ‘yan jam’iyyarmu da-dama sun fusata a zaben fitar da gwanin da aka yi a 2018, amma saboda mun yi amanna da manufofin jam’iyyar, mu ka zauna mu ka yi wa jam’iyya aiki domin ta samu nasara.”

Yar’adua ya ke cewa duk da sabanin da aka samu, basu sauya-sheka ba, sun yi wa APC aiki a zaben 2019.

Tsohon sojan ya kara da cewa dole a saurari korafe-korafensu, idan har ana so uwar-jam’iyya ta iya gudanar da danyen zaben shugabanni na kasa a cikin karshen shekarar nan mai-ci.

“Idan ba a yi sulhu da ‘ya ‘yan jam’iyya da su ka yi fushi ba, ba za ayi zaben shugabanni ba.”

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Kanal Abdul’aziz Musa Yar’adua mai ritaya ya bayyana wannan ne a ranar Talata, 30 ga watan Yuni, 2020.

A 2015, ‘dan siyasar da aka fi sani da Audu Soja ya nemi takarar gwamna da ‘dan majalisa amma duk bai dace ba. A 2011, ya tsaya a matsayin mataimakin Lado Dan Marke a jam’iyyar CPC.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel