Cutar korona ta hallaka mutum 475 a Najeriya - NCDC

Cutar korona ta hallaka mutum 475 a Najeriya - NCDC

- A yanzu cutar korona ta bulla a jihohi 35 na Najeriya da kuma babban birnin kasar na Tarayya

- Jihar Legas ce ke jan ragama inda ta harbi mutum 7,896, mutum 1,382 suka warke sai kuma mutum 108 da suka kwanta dama

- A halin yanzu cutar ta harbi mutum 18,480, sai kuma mutum 6,307 da suka samu waraka, yayin da mutum 475 suka riga mu gidan gaskiya

Ya zuwa yanzu dai an samu bullar cutar korona a jihohi 35 na Najeriya ciki har da babban birnin tarayya kamar yadda kididdigar hukumar dakile cututtuka masu yaduwa a kasar NCDC ta tabbatar.

Tabbas mahukuntan lafiya na ci gaba fadi-tashi ba dare ba rana domin dakile yaduwar cutar korona, sai dai fa lamarin ya ci tura domin kuwa cutar na ci gaba da bazuwa tamkar wutar daji.

Taskar bayanai ta NCDC a ranar Alhamis, 118 ga watan Yuni, ta ce cutar ta harbi mutane 18,480 yayin da tuni an sallami mutum 6,307 daga cibiyoyin killace masu cutar bayan da suka warke.

Jadawalin NCDC ya tabbatar da cewa ya zuwa yanzu dai cutar corona ta hallaka mutum 475 a fadin kasar.

Da misalin karfe 11.43 na ranar Alhamis da daddare, NCDC ta sanar da cewa an gano karin sabbin mutane 745 da cutar ta harba a fadin Najeriya.

Shugaban NCDC; Dr. Chikwe Ihekweazu
Shugaban NCDC; Dr. Chikwe Ihekweazu
Asali: Facebook

Sabbin mutane 745 da cutar ta harba cikin jihohin 21 sun kasance kamar haka: Lagos(280), Oyo(103), Ebonyi(72), FCT(60), Imo(46), Edo(34), Delta(33), Rivers(25), Kaduna(23), Ondo(16), Katsina(12), Kano(10), Bauchi(8), Borno(7), Kwara(5), Gombe(4), Sokoto(2), Enugu(2), Yobe(1), Osun(1), Nasarawa(1).

KARANTA KUMA: Cika shekaru 45: Shugaba Buhari ya aika da sakon taya murna na musamman ga Yahaya Bello

Har ila yau jihar Legas ce a kan sahu na gaba ta fuskar yawan mutanen da cutar ta harba, sai kuma birnin Abuja a mataki na biyu yayin da jihar Kano ta biyo bayansu a mataki na uku.

Ga jerin adadin mutanen da cutar korona ta hallaka a jihohin Najeriya da cutar ta bulla:

Lagos (108),

Abuja (28),

Kano (50),

Ogun (15),

Kaduna (10),

Katsina (22),

Sokoto (14),

Edo (31),

Borno (30),

Ebonyi (1),

Osun (4),

Oyo (9),

Ekiti (2),

Delta (17),

Rivers (26),

Nasarawa (6),

Yobe (8),

Zamfara (5),

Jigawa (6),

Ondo (15),

Kebbi (6),

Kwara (6),

Gombe (13),

Bauchi (11),

Imo (3),

Filato (5),

Bayelsa (3),

Enugu (5),

Anambra (9),

Neja (2),

Akwa Ibom (2),

Adamawa (4).

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel