Yanzu-yanzu: Buhari zai sake jawabi ga yan Najeriya gobe

Yanzu-yanzu: Buhari zai sake jawabi ga yan Najeriya gobe

Shugaba Muhammadu Buhari zai yi jawabi ga yan Najeriya ranar Litinin, 18 ga Mayu domin sanar da matakin gaba kan lamarin sassauta dokar hana fitan da aka sa domin takaita yaduwar cutar Korona.

Jagoran kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar COVID-19, Aliyu Sani, ya bayyana hakan a hirar da ya yi a tashar ChannelsTV da daren Lahadi.

A cewarsa, Buhari zai yanke ko za'a kara sassauta dokar hana fitan karo na biyu.

Za ku tuna cewa a karo na daya, an amince bankuna, masana'antun sarrafa kayan abinci, kantunan sayar da kayayyakin masarufi su bude.

Hakazalika an amince manyan ma'aikatan gwamnati su koma bakin aiki.

Saurari cikakken rahoton...

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng