Mataimakin shugaban jam’iyyar APC da diyarsa sun fada hannun barayin mutane a Kaduna

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC da diyarsa sun fada hannun barayin mutane a Kaduna

Wasu gungun miyagun yan bindiga sun yi awon gaba da mataimakin shugaban jam’iyyar APC reshen jahar Kaduna, Shu’aibu Idris tare da diyarsa.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito yan bindigan sun sace Idris da diyar tasa ce a ranar Laraba, 13 ga watan Mayu a garin Zaria na jahar Kaduna.

KU KARANTA: Sarkin Musulmi ya umarci Musulmai su yi addu’o’in ganin bayan Corona a ranar Alhamis

Shugaban jam’iyyar APC ta jahar Kaduna, Commodore Emmanuel Jekada ne ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Alhamis, inda yace har cikin gida yan bindigan suka bi Idris.

“Yan bindigan sun sace Idris da diyarsa ne daga gidansa dake kwanar zango a kan babbar hanyar Zaria zuwa Kaduna.” Inji shugaban APC Emmanuel Jekada.

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC ya fada hannun barayin mutane a Kaduna
Shuaibu Idris Hoto:Shafin gwamnan Kaduna
Asali: Twitter

Jekada ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, sa’annan ya kara da cewa jam’iyyar ta fara kokorin ganin an ceto Idris da diyarsa daga hannun miyagun.

Sai dai har zuwa lokacin tattara wannan rahoton rundunar Yansandan jahar Kaduna bata ce uffan game da lamarin ba.

Idan za’a tuna a ranar Litinin, 12 ga watan Mayu ma wasu gungun yan bindiga sun kai hari karamar hukumar Kajuru ta jahar Kaduna inda suka kashe mutane 8.

Yan bindigan sun yi kashe kashen ne a wasu munanan hare hare da suka kai wasu kauyuka guda uku dake makwabtaka da juna da suka hada da Idanu, Mkyali da Bakin-Kogi.

A yayin wannan hari, sun kona gidaje da gonakai da dama. Wannan hari kuma ya zo ne jim kadan bayan wani hari da yan bindiga suka kai kauyen Gonna-Rogo, duk a cikin Kajuru.

A wannan hari na Gonna-Rogo, sun kashe akalla mutane 15, tare da jikkata wasu da dama, kamar yadda mazauna kauyen suka tabbatar.

A wani labari, Gwamnatin jahar Zamfara ta sanar da mutuwar manyan sakatarorinta guda biyu a cikin kwanaki biyu sakamakon wata yar gajeruwar rashin lafiya da suka yi fama da ita.

Manyan jami’an gwamnatin da suka mutu sun hada da Alhaji Yawale Dango, babban sakatare a ofishin shugaban ma’aikatan jahar.

Sai kuma Alhaji Ahmed Sale, babbana sakatare a ma’aikatan gidaje da cigaban biranen jahar Zamfara. Sale ya rasu a ranar Talata, yayin da Dango ya rasu a ranar Larabar da ta gabata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel