Goman karshe: An bude Masallatan kasar Iran domin gudanar da Sallolin dare

Goman karshe: An bude Masallatan kasar Iran domin gudanar da Sallolin dare

A farkon makon nan da muke ciki ne kasar Iran ta sanar da bude Masallatan kasar da aka rufe bayan bullar annobar korona.

Duk da tsoron kwayar cutar korona da ake yi a kasar Iran, dubun dubatar Iraniyawa a ranar Laraba sun yi dandazo wajen cika Masallasatai domin gabatar da Salloli a cikin kwanakin karashe na watan Ramadan mai alfarma.

A Masallacin Reihanat al-Hussein da ke yammacin Tehran, an ga masallata cikin takunkumin fuska yayin da suke zaune nesa da junansu domin gudanar da ibadu.

Masallatan da suka hada da Maza da Mata, yara da manya, sun kasance cikin tsari da biyayya ga matakan da aka gindaya domin kare kai da kuma dakile yaduwar annobar korona.

Akwai ma'aikaci da ke kewayawa a harabar Masallacin ya na fesawa Masallata ruwan maganin da ke kashe kanan kwayoyin cuta.

Kazalika, akwai jami'an tsaro da ke lura da jama'a tare da umartarsu su nesanci juna idan takin da ke tsakanins bai kai wanda doka ta ambata ba.

Goman karshe: An bude Masallatan kasar Iran domin gudanar da Sallolin dare

Masallacin Reihanat al-Huseein
Source: UGC

"Tabbas mun damu da bullar wannan annoba, hatta iyalina a cikin damuwa suke," a cewar wani mutum mai suna Mahmoudi yayin hira da manema labarai a harabar Masallaci.

Mahmoudi ya cigaba da cewa, "iyalina sun shiga damuwa lokacin da na sanar da su cewa zan fita zuwa Masallaci, amma sai na daukar musu alkawarin cewa zan kiyaye dukkan matakan kare kai da aka saka.

DUBA WANNAN: Za a cigaba da sallar Juma'a a Masallatan jihar Jigawa

"Na ji dadin ganin yadda kowa a Masallacin ke biyayya ga tsarin nesanta, ba don haka ba, da ni ma ba zan zauna a Masallacin ba, gida zan koma," a cewarsa.

Tun a cikin watan Maris kasar Iran ta rufe Masallatanta a matsayin daya daga cikin matakan dakile yaduwar annobar korona, wacce ta bulla da karfinta a yankin gabas ta tsakiya.

Amma, kasar ta bude Masallatan domin bawa jama'a damar riskar daren Laylatul Qadri, wanda aka saukarwa annabi Muhammad Al-Qur'ani a cikinsa.

A ranar 19 ga watan Fabrairu aka fara samun bullar annobar korona a birnin Qom na mabiya Shi'a kafin daga bisani annobar ta yadu, cikin gaggawa, zuwa sauran jihohin kasar 31.

Ya zuwa wannan lokaci, annobar korona ta kashe kusan mutane 6,800 a kasar Iran.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel