Yanzu-yanzu: Majalisar dattijai ta yi sabon kakaki

Yanzu-yanzu: Majalisar dattijai ta yi sabon kakaki

- Shugaban majalisar dattijan Najeriya, Ahmad Lawan ya bayyana Sanata Ajibola Basiru a matsayin sabon kakakin majalisar dattijan

-Basiru ya maye gurbin sanata Adebayo Adeyeye wanda shine tsohon kakakin kafin kotu ta kwace kujerarsa

- Kamar yadda shugaban majalisar ya bayyana, za su ci gaba da aiki daga gida tare da zuwa zauren majalisar matukar bukatar hakan ta taso

Shugaban majalisar dattijan Najeriya, Ahmad Lawan ya bayyana sanata daga jihar Osun, Ajibola Basiru a matsayin sabon shugaban kwamitin yada labarai na majalisar.

Basiru zai dasa daga inda Sanata Godiya Akwashiki ta tsaya a matsayin mukaddashin kakakin majalisar.

Ta ci gaba da aiki a matsayin kakakin majalisar dattijan ne tun bayan da aka kwace kujerar Adebayo Adeyeye a kotu.

Akwashiki sanata ce a karkashin jam'iyyar APC daga jihar Nasarawa.

Ba kakakin majalisar kadai zai tsaya ba, zai kasance shugaban kwamitin majalisar na daukar aiki da kwadago.

Sanata Biodun Olujimi ta jihar Ekiti karkashin jam'iyyar PDP ce ta zama shugabar kwamitin majalisar mai kula da 'yan Najeriya da ke kasashen ketare da kuma kungiyoyin taimakon kai da kai.

Lawan ya bada wannan sanarwar ne a yayin tashi zaman majalisar na yau Talata, jaridar Premium Times ta wallafa.

A jawabinsa na tashi daga zaman majalisar, Lawan ya mika godiyarsa ga abokan aikinsa a kan jajircewarsu.

Yanzu-yanzu: Majalisar dattijai ta yi sabon kakaki
Yanzu-yanzu: Majalisar dattijai ta yi sabon kakaki
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kwamandan Soji ya nada kansa shugaban kasa a Libya

Ya tabbatar da cewa 'yan majalisar za su sake taruwa don aminta da kasafin kudin shekarar 2020 da aka sake dubawa.

Za su yi hakan ne bayan majalisar zartarwa ta sake kiransu.

Ya sake umartar dukkan kwamitin da ke majalisar da su ci gaba da ayyukansu ko bayan an dakatar da zaman majalisar.

Shugaban majalisar ya kara da bayyana cewa majalisar za ta dakatar da zamanta, amma 'yan majalisar za su ci gaba da ayyukansu daga gida.

Wannan na bayyana cewa, babu ranar sake zama a majalisar kuma 'yan majalisar za su iya haduwa a duk lokacin da hakan ta taso.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel