Majalisar wakilai ta gimtse hutun da ta tafi bayan barkewar annobar covid-19
Majalisar waikilai ta tsayar da ranar Talata, 28 ga watan Afrilu, 2020, a matsayin ranar da zata dawo daga hutun da ta tafi.
Jaridar 'OderPaperNG' ta rawaito cewa ta ga sakonnin sanarwa da aka aikewa mambobin majalisar da yammacin ranar Lahadi.
A cikin sakon sanarwar, mai dauke da sa hannun Patrick A. Giwa, magatakardar majalisa, an shawarci sauran hadiman mambobin majalisa su cigaba da zama a gida zuwa sanarwa ta gaba.
A cewar sanarwar, "za a yi zaman majalisar ne bisa biyayya ga shawarwarin hukumar NCDC da kuma wasu sabbin matakai da majalisa ta dauka."
Sanarwar ta bayyana cewa; "mu na sanar da dukkan mambobin majalisar wakilai cewa za a dawo zaman majalisa a ranar Talata, 28 ga watan Afrilu, da misalin karfe 10:00 na safe.

Asali: UGC
"Ana shawartar mambobi a kan su kiyaye da sabon lokacin da aka bayyana a matsayin ranar dawowa daga hutun.
"Za a gudanar da zaman majalisa bisa kiyaye matakan da hukumar NCDC ta shimfida da kuma wasu karin matakai da majalisa ta dauka, wanda za a aika wa kowanne mamba.
DUBA WANNAN: Magoya bayan Buhari sun bayyana wanda su ke so ya maye gurbin marigayi Abba Kyari
"Ana shawartar sauran ragowar hadiman mambobin majalisa a kan su cigaba da aiki daga gida matukar ba neman mutum aka yi har zuwa fitowar sanarwa ta gaba."
A ranar 24 ga watan Maris ne majalisar wakilai ta tafi hutu sakamakon barkewar annobar covid-19.
Ana ganin cewa akwai harkokin da suka shafi annobar covid-19, musamman batun kudaden tallafi, da ake bukatar amincewar majalisa a kan yadda za a yi amfani da su.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng