Jerin kasashen Afirka da suka fi yawan masu cutar Korona – WHO

Jerin kasashen Afirka da suka fi yawan masu cutar Korona – WHO

- Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce an samu mutum fiye da 21,000 da suka kamu da Coronavirus a nahiyar Afirka

- Hukumar ta ce mutum 5,000 sun warke yayin da 1,000 sun mutu sakamakon annobar

- Rahoton da WHO ta wallafa ya nuna cewa mutum 3,158 sun kamu a Afirka ta Kudu, 2,629 a Algeria, 1,042 a Ghana sai 1,016 a Kamaru

Sama da mutane 21,000 aka ruwaito sun kamu da coronavirus a nahiyar Afirka, 5,000 sun warke yayin da 1,000 sun mutu a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO.

Hukumar ta wallafa kididigan yadda mummunar cutar ta yadu a mahiyar Afirka da adadin wanda cutar ta kashe zuwa ranar 2 ga watan Afrilu kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

A jerin kasashen da ta wallafa, WHO ta nuna cewa an samu mutum 541 da suka kamu da cutar a Najeriya wanda hakan ke nuna cewa an wallafa rahoton ne kafin hukumar NCDC ta Najeriya ta fitar da sabbin alkallumanta.

DUBA WANNAN: An kama mutumin da ya haike wa matarsa har ta mutu a Jigawa

Rahoto game da yaduwar cutar da NCDC ta fitar a daren ranar Asabar 24 ga watan Afrilu da karfe 11.3O ya nuna cewa mutum 1O95 ne suka kamu da cutar a kasar.

Mutum 2O8 sun warke an sallame su yayin da mutum 32 cutar da kashe tun bullar ta a kasar.

Rahoton da WHO ta wallafa ya nuna cewa mutum 3,158 sun kamu a Afirka ta Kudu, 2,629 a Algeria, 1,042 a Ghana sai 1,016 a Kamaru.

Ga dai sabon kididdigar yadda cutar ta yadu a kasashen nahiyar Afirka a kasa zuwa ranar 24 ga watan Afrilu.

Jerin kasashen Afirka da suka fi yawan masu cutar Korona – WHO

Jerin kasashen Afirka da suka fi yawan masu cutar Korona – WHO. Mallakin Hoto - WHO
Source: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel