Covid-19: 'Yan jihar Filato 6 ne suka tsere daga cibiyar killacewa ta jihar Nasarawa

Covid-19: 'Yan jihar Filato 6 ne suka tsere daga cibiyar killacewa ta jihar Nasarawa

- Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce mutum biyar 'yan asalin jihar Filato ne suka tsere daga cibiyar killacewa ta jihar Nasarawa

- Ya sanar da hakan ne yayin jawabin bude taron sarakunan gargajiya da na addinai a gidan gwamnatin jihar da ke Lafia a jiya

- Ya ce a halin yanzu za su dinga killace mutanen da suka dawo daga Legas ko Kano na kwanaki 14 don hana yaduwar cutar coronavirus a jihar

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce mutum biyar 'yan asalin jihar Filato ne suka tsere daga cibiyar killacewa ta jihar Nasarawa.

Ya sanar da hakan ne yayin jawabin bude taron sarakunan gargajiya da na addinai a gidan gwamnatin jihar da ke Lafia a jiya Litinin.

Ya ce an kama mutum biyar da suka tsere zuwa daji bayan abun hawansu ya tsaya a wani kauye da ke tsakanin jihar Nasarawa a hanyarsu ta zuwa Jos jihar Filato, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Wasu 13 daga ciki sun yi ikirarin cewa sun taho ne daga jihar Nasarawa za su je Lafia, babban birnin jihar.

Gwamnan ya tabbatar da cewa za a killacesu da gaggawa bayan sun isa babban birnin jihar.

Ya ce a halin yanzu za su dinga killace mutanen da suka dawo daga Legas ko Kano na kwanaki 14 don hana yaduwar cutar coronavirus a jihar.

Covid-19: 'Yan jihar Filato 6 ne suka tsere daga cibiyar killacewa ta jihar Nasarawa
Covid-19: 'Yan jihar Filato 6 ne suka tsere daga cibiyar killacewa ta jihar Nasarawa
Asali: UGC

KU KARANTA: Hankula sun tashi a Kano bayan mutum 150 sun rasu a cikin kwana 3

Gwamnan ya ce a halin yanzu an killace mutum 43 da ke dawowa daga jihar Legas a Akwanga a kan hanyarsu ta zuwa Shendam ta jihar Filato.

Ya bayyana cewa, da hadin guiwar gwamnatin jihar Filato din, an raka matafiyan har Jos inda aka killacesu.

A wani labari na daban, a kalla mutum 150 ne suka rasa rayukansu tsakanin ranar Juma'a da Asabar na makon da ya gabata a garin Kano.

Wannan tururuwar birne jama'ar ne ya saka tsananin tsoro da fargaba a zukatan mazauna jihar don basu san takamaiman abinda ya jawo mutuwar ba.

Masu hakar kaburbura a makabartun birnin Kano sun ce yawan gawawwakin da aka kai makabartun ya fi yadda suka saba birnewa kafin barkewar annobar Coronavirus.

Hukumomi a jihar Kano, shugabanni, iyalan mamatan da kuma ma'aikatan lafiya na jihar sun bada labari mabanbanta game da mace-macen.

Wakilin jaridar Daily Trust ya bayyana cewa wannan ci gaban ya matukar girgiza zukatan mazauna birnin Kano don sun fara zargin cewa annobar ce ke dibar rayuka a cikin jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel