An yi wa Abba kyari sadakar uku da ta bakwai a Borno (hotuna)

An yi wa Abba kyari sadakar uku da ta bakwai a Borno (hotuna)

- An yi wa tsohon shugaban ma’aikatan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Mallam Abba Kyari addu’ar uku da bakwai

- Iyalan sun hada ranakun addu’ar ne domin guje ma cunkosan jama’a, yan zuwa ta’aziyya

- Gwamnan jahar Borno, Babagana Umara Zulum ma ya halarci taron

Iyalan marigayi tsohon shugaban ma’aikatan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Mallam Abba Kyari, sun gudanar da taron addu’ar uku da bakwai domin mamacin.

An tattaro cewa iyalan sun hada ranakun addu’ar ne domin guje ma cunkosan jama’a, yan zuwa ta’aziyya.

Daga cikin wadanda suka halarci taron addu’ar harda gwamnan jahar Borno, Babagana Umara Zulum.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai Malam Abba Kyari ya rasu bayan fama da cutar korona ta kimanin makonni hudu.

An yi wa Abba kyari sadakar uku da ta bakwai a Borno (hotuna)

An yi wa Abba kyari sadakar uku da ta bakwai a Borno
Source: Twitter

An yi wa Abba kyari sadakar uku da ta bakwai a Borno (hotuna)

Gwamna Zulum ma ya halarci taron addu'ar
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: An sake sallamar karin masu COVID-19 su 4 a Lagas

A halin da ake ciki, mun ji cewa wani babban lauya a Najeriya, Femi Falana, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta gudanar da bincike a kan mutuwar shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari.

Babban lauyan ya nemi gwamnatin da ta gaggauta aiwatar da bincike a kan ababen da suka dabaibaye jinya da kuma mutuwar marigayi Kyari.

Falana ya ce bukatar aiwatar da binciken ta zo ne duba da yadda aka yi jinyar marigayi Kyari a wani asibitin kudi sabanin yadda Ministan Lafiya, Osagie Ehanire ya shar'anta.

A baya dai Mista Ehanire ya ce babu wani asibitin kudi a fadin kasar nan da aka yiwa lamunin duba lafiyar duk wani wanda cutar coronavirus ta harba kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Lauya Femi ya ce wannan ce madogararsa ta neman gwamnati ta gudanar da binciken gaggawa kan mutuwar mai lura da al'amuran ma'aikatan fadar shugaban kasa da ajali ya katsewa hanzari.

Lauyan ya ce duba lafiyar marigayi Mallam Kyari da aka yi a asibitin kudi ya sabawa ka'aidoji da kuma sharuddan da aka gindaya kan annobar cutar covid-19.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel