Gwamna Zulum ya roki afuwar mutanen jihar Borno

Gwamna Zulum ya roki afuwar mutanen jihar Borno

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya nemi afuwar mutanen jihar Borno a kan raunin da yake da shi da kuma gazawarsa yayin da yake jagorantar gwamnatin jihar.

A ranar Talata ne Zulum ya rufe wasu gidajen sayar da man fetur guda 10 da ke Maiduguri bayan samunsu da laifin boye man fetur.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa wasu gidajen sayar da man fetur a jihar Borno sun boye mai tare da sayar da shi a farashi mai tsada tun bayan sanarwar matakan dakile yaduwar annobar cutar covid-19.

Hakan ne yasa gwamna Zulum da kansa ya kai wata ziyarar bazata a irin gidajen man da ake zargi da aikata hakan domin tilasta su budewa tare da sayarwa da jama'a man a kan farashin da gwamnati ta yanke.

Zulum ya nemi afuwar mutanen jihar Borno ne ranar Alhamis yayin da yake gabatar da jawabi kai tsaye ga jama'ar jiharsa daga fadar gwamnatin jihar Borno da ke Maiduguri. Gwamnan ya ce azarbabinsa da sauran gazawarsa, halaye ne na duk wani mutum mai damuwa da halin da jama'a ke ciki ko kuma kyamar ganin an yi ba daidai ba.

Gwamna Zulum ya roki afuwar mutanen jihar Borno
Gwamna Zulum
Asali: UGC

A cewar gwamna Zulum, ya kan gaza hadiye fushinsa duk lokacin da yada wani yana kokarin amfani da wata dama domin zaluntar talakawa ko jefa su a cikin wahala.

Ya bayyana cewa tunda ya hai mulki gwamnatinsa ke aiki ba dare ba rana don ganin ta dawo da zaman lafiya a jihar.

DUBA WANNAN: Shekau ya saki sabon sako bayan sojojin kasar Chadi sun kashe masa dumbin mayaka

"Ina sauraron duk abinda jama'a suke fada kuma zan yi kokari wajen yin aiki da wasu daga cikin shawarwarin da ake bani domin inganta aiyukan gwamnati ko kuma inganta rayuwar jama'a.

"Duk da bana rike da kowa a cikin zuciyata, ina mai neman afuwarku, ku gafarci gazawata. Babban burin gwamnatina shine ta saka jama'a farko a duk abinda za ta yi.

"Kofofinmu a bude suke domin tuntuba ko kuma bayar da wata shawara mai muhimmanci da za ta kawo mana cigaba.

"Ina godiya ga kowa da kowa bisa kulawarku gareni da gwamnati. Ina mai tabbatar muku cewa za mu yi iyakar kokarinmu domin ganin mun inganta rayuwar jama'armu da kawowa jiharmu cigaba.

"Mu cigaba da addu'ar neman dawowar zaman lafiya a jiharmu tare da rokon kariyar Allah daga annobar cutar covid-19," a cewar Zulum.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel