Kwanaki 8 bayan kamuwa da cutar Coronavirus, shugaban asibitin jami'ar Ibadan ya warke

Kwanaki 8 bayan kamuwa da cutar Coronavirus, shugaban asibitin jami'ar Ibadan ya warke

Bayan kwanaki takwas a killace kuma yana jinya, shugaban asibitin jami'ar Ibadan, jihar Oyo, Farfesa Jesse Otegbayi, ya warke daga cutar Coronavirus.

Shugaban sashen hulda da jama'a na asibitin, Toye Akinrinola, ya tabbatar da cewa gwajin da aka jiwa maigidanshi na baya-baya na nuna cewa ya warke daga cutar.

Akinrinlola ya ce sakamakon gwajin ya fito ne misalin karfe 3:45 na rana kuma hakan ya farantawa yan'uwa da abokan arziki rai.

Kwanaki 8 bayan kamuwa da cutar Coronavirus, shugaban asibitin jami'ar Ibadan ya warke
Kwanaki 8 bayan kamuwa da cutar Coronavirus
Asali: UGC

KU KARANTA: Adadin wadanda suka kamu da Coronavirus a duniya ya kai miliyan daya

A makon da ya gabata, mun kawo muku rahoton cewa shugaban asibitin da ke jami’ar Ibadan, Farfesa Jesse A Otegbayo ya tabbatar da cewa ya kamu da cutar Coronavirus a halin yanzu.

Jesse A Otegbayo ya bada wannan sanarwa ne a wani jawabi da ya fitar da hannunsa. Jesse A Otegbayo ya kamu da wannan cuta ne a taron da su ka yi kwanaki.

Farfesa Otegbayo ya ce bayan sun fara gudanar da wani taro na shugabannin asibitin UCH a makon jiya, sai su ka fahimci Abokin aikinsu ya kamu da COVID-19.

Otegbayo ya shaidawa ‘Yan jarida cewa wannan ya sa su ka dakatar da taron, sannan kuma aka yi wa wannan Bawan Allah gwaji, inda aka tabbatar ya kamu da cutar.

A dalilin haka, Jesse A Otegbayo da sauran Likitoci su ka killace kansu, sannan aka yi masu gwaji. Bayan sakamako ya fita, an gane cewa cutar ta kama Likitan

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel