Duk da bashin N105bn da ake bin jihar, gwamnatin Bauchi ta karbi bashin N3.5bn don sayan motoci

Duk da bashin N105bn da ake bin jihar, gwamnatin Bauchi ta karbi bashin N3.5bn don sayan motoci

Duk da bashin da ake bin jihar Bauchi na kimanin ₦105 billion, gwamnatin jihar Bauchi ta sake karban bashin ₦3.5 billion domin sayen motoci ga jami'an gwamnatin jihar, Premium Times ta ruwaito.

Banki ta biya kudin cikin asusun bakin kamfanin Adda Nigeria Limited, kamfani da gwamna Mohammed Bala ke da hannun jarin kashi 20 cikin 100.

A ranar 21 ga Agusta, 2019, bankin ta rubuta wasika ga kamfanin kan bashin ₦3.5 billion domin sayen motoci 105 ga wasu jami'ai da ma'aikatun gwamnatin jihar Bauchi kuma za'a biya cikin watanni 36.

Duk da bashin N105bn da ake bin jihar, gwamnatin Bauchi ta karbi bashin N3.5bn don sayan motoci

gwamnatin Bauchi ta karbi bashin N3.5bn don sayan motoci
Source: Facebook

A baya mun kawo muku rahoton cewa Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya baiwa kamfanin da shi ne diraktanta kwangilan kudi sama da bilyan uku da rabi , kuma hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa ga masu rike da mukaman mulki, Premium Times ta ruwaito.

Kwangilar ita ce sayan motoci 105 domin amfanin gwamnan da wasu jami'an gwamnatin jihar.

Kuma duk da hakan, ana cece-kucen cewa kamfanin bata wanzar da kwangilan kamar da aka bukata ba.

Jami'an da suka san lamarin kwangilan sun bayyana cewa kamfanin Adda Nigeria Limited, aka baiwa kwangilan kuma gwamnan jihar Bauchi na da hannun jarin kashi 20 cikin 100 a kamfanin.

Gwamnan wanda tsohon minista birnin tarayya ne ya lashe zaben jihar ne saboda kukan mutan jihar Bauchi kan magabacinsa, Mohammed Abubakar.

Gabanin zamansa gwamna, Bala Mohammed na gurfanar gaban kotu kan tuhumar almundahanan kudade lokacin da yake minista.

Hukumar EFCC ta shigar da shi kotu kan zargi-zargi shida na almundahana da babakekere. Amma ya musanta dukkan zargin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel