Farashin danyen mai ya tashi bayan harin da Iran ta kai kan sojin Amurka
Rahotanni sun nuna cewa farashin danyen mai ya yi tashin gwauron zabi bayan da wasu makamai masu linzami suka fadawa wasu sansanonin sojin Amurka biyu da ke kasar Iraki.
Farashin danyen mai rukunin Brent ya tashi da kaso 1.4 cikin 100 inda ake sayarwa kan dala 69.21 kowace gangar mai daya a kasuwar mai ta Asia.
An kuma tattaro cewa su kansu ma ma'adinan kasa kamar gwal da kudin Japan Yen sun tashi bayan da aka kai harin.
Har ila yau hannun jari a duniya ya yi kasa sakamakon rikicin da ake yi a yankin gabas ta tsakiya.
Kasuwar hannayen jari ta Japan, Nikkei 225 ta yi kasa da kashi 1.3 cikin 100 yayin da kasuwar hannayen jari a Hong Kong, Hang Seng ta yi kasa da kashi 0.8 cikin 100.
Iran ta harba rokoki 20 sansanin Sojin Amurka dake Iraqi domin mayar da martani kan kisan babban kwamandan Iran, Qassem Soleimani, da Amurka tayi ranar Juma'a.
KU KARANTA KUMA: Iran ta ce Amurkawa 80 aka kashe a harin makamai masu linzami da ta kai
Sansanin Ayn Al Asad da Sansanin Erbil Asad ne aka harba manyan rokokin misalin karfe 5:30 na yammacin Talata sannan kuma akalla sojojin Amurka 80 sun hallaka.
Hukumar tsaron Iran ta gargadi Amurka kan kokarin ramawa. Sun sanar da hakan ne ta wabi jawabi a tashar gwamnatin Iran IRNA.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng