Fitattun jaruman Indiya 6 da suka taba ziyartar dakin Allah

Fitattun jaruman Indiya 6 da suka taba ziyartar dakin Allah

Aikin hajji dai yana daya daga cikin shika-shikan musulunci wanda Allah (SWT) ya farlanta a kan wadanda suke da halin zuwa aikin hajjin. Kamar takwarorinsu na sauran kasashe, akwai wasu daga cikin jaruman Bollywood da Allah ya bawa ikon sauke faralin. Ga jerin sunayensu kamar yadda Bbc hausa ta ruwaito.

1) Amir Khan

Amir Khan yana daya daga cikin shahararun jarumin Bollywood wanda suka sami ikon zuwa aikin Hajji.

Jarumin ya sauke faralin ne a shekarar 2012 tare da mahaifiyarsa Zainat Hussain wanda dama ya jima da daukar alkawarin cewa zai kai ta Makka don sauke faralin, hakan yasa jarumin ya cika alkawarinsa.

Amir Khan ya fito a manyan fina-finai da dama duk da cewa yanzu girma ya fara zuwa masa.

2) AR Rehman

AR Rehman shahararen mawaki ne kuma mai kida a masana'antar fina-finan na Indiya wanda ya samu ikon sauke farali har sau biyo. Ya fara zuwa aikin Hajji na farko a shekarar 2004 sannan ya sake komawa a 2006.

Shahararen mawakin ya taba shaidawa manema labarai cewa yana matukar farin ciki da Allah ya bashi ikon sauke faralin.

3) Sana Khaan

Sana Khaan jarumar fina-finai ce kuma mai rawa kuma a wasu lokuta takan fito a talle. jarumar ta fito a fina-finai 14 da kuma talle guda 50. Iyayenta musulmai ne kuma ta girma a garin Mubai.

Khaan ta samu ikon sauke farili a shekarar 2017.

Ta fito a fina-finai kamar su Bombay to Goa, Jai Hoi,Wajah Tum Ho da sauransu.

4) Kader Khan

Kader Khan yana daya daga cikin tsaffin jaruman Bollywood wanda ya shahara wajen barkwanci kuma a wasu lokutan ma yakan rubuta fim.

Ya fara fitowa a fina-finai ne a shekarar 1973.

Jarumin ya sami ikon sauke farali a shekara 2014 tare da 'ya'yansa maza biyu.

5) Mohammad Rafi

Mohammed Rafi shahararen mawaki ne a Bollywood. Ya yi wakoki fiye da 28 daga shekarar 1944 - 1980.

Ya tafi Makka don yin aikin Hajji a shekarar 1970 tare da matarsa Bilkis Rafi da kuma dan uwansa Mohammed Din.

Wasu daga cikin fitattun wakokinsa sun hada da Kya Hua Tera Wada da Dard-e-dil dard-e-jigar.

6) Dilip Kumar

Cikaken sunansa Muhammed Yusuf Khan kuma a yanzu yana da shekaru sama da 90 a duniya.

Bayan fitowa a matsayinsa na jarumin fim, yana kuma rubuta labaran fim kuma mai gwagwarmayar kare hakkin mutane ne.

Kumar ya fara zuwa Umrah ne a 2013 kana a shekarar 2014 suka tafi aiki Hajji tare da matarsa Saira Banu.

Wasu daga cikin fina-finansa sun hada da Kranti da Saudagar da Mashaal da sauransu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel