An yi rijistan almajirai 7,000 don sanyasu a makarantun Boko a jihar Neja

An yi rijistan almajirai 7,000 don sanyasu a makarantun Boko a jihar Neja

Gwamnatin jihar Neja ta dauki sunayen Almajirai akalla 7000 karkashin shirin ilmantar da yara, tare da gudunmuwar bankin duniya.

An samar da shirin ne domin rage yawan kananan yara maras zuwa makaranta a Najeriya.

Shugaban ma'aikatar ilmin kasa da sakandare na jihar Neja, Dakta Isa Adamu, ya sanar da hakan ne lokacin da ya kai ziyara wasu makarantu a Minna domin duba yadda malaman almajiran ke bada hadin kai.

Adamu ya bayyana cewa za'a rika ciyar da Almajiran sau biyu a mako domin basu damar mayar da hankali wajen karatu.

Ya kara da cewa Almajiran dake rijista na karuwa wanda ke nuna amincewarsu da shirin.

Ya bayyana farin cikinsa kan yadda makarantun Almajiran da ya ziyarta suke bada hadin kai da kuma taimakawa wajen ganin cigaban shirin a jihar Neja.

A cewarsa, ana shirye-shiryen kara albashin malaman shirin domin kara musu karfin gwiwa.

Jihohi 17 ke musharaka cikin shirin na bankin duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel