Yadda Dangote ya zama dan Afirka tilo cikin jerin mutane 100 mafi arziki a duniya

Yadda Dangote ya zama dan Afirka tilo cikin jerin mutane 100 mafi arziki a duniya

Jerin manyan biloniyoyi na duniya na shekarar da ta gabata ya fita kuma Aliko Dangote ne ya bayyana a na 96 da kiyasin kusan dala biliyan 14.8. Ya wuce wancan jerin na 2018 inda ya bayyana a na 103.

A cikin shekaru takwas da suka gabata, Dangote ne ya kasance mafi arziki a nahiyar Afirka kuma shine a kan gaba a biloniyoyi 100 na Najeriya, kamar yadda Blomberg ta ke saki duk shekara.

Jeff Bezos ne mutum mafi arziki a duniya, Bill Gates da Bernard Arnault ne suke a sahun na biyu da na uku a duniya. Warren Buffett ne na hudu a jerin masu kudin duniya.

Matakin da Dangote ya kai a sabuwar mujallar Blomberg din yayi wa matakin da jaridar Forbes ta saka shi fintinkau. Duk da kuwa ya tsare matakin na farko a tun daga shekaru takwas da suka gabata har zuwa yanzu.

DUBA WANNAN: Kano ta dara London sanyi - NIMET

Mashahurin mai kudin Afirka din shine ke juya akakar kasuwancin kamfanonin Dangote. Kamfaninsa na siminti dake Legas ne babban kamfanin siminti dake Afirka. Yana Samar da naira biliyan 901.2 na kudin shiga a 2018. Kamfanin babban dan kasuwar na samar da sukari, gishiri, fulawa, taki da sauransu.

Idan ba zamu manta ba, Aliko Dangote ya zama na shida a duniya dake bada kyauta ko zakka. A wannan jerin, an duba bangaren kasuwanci, yawan dukiya, da sauransu.

An gano hakan ne bayan da gidauniyar Dangote ta haye mataki na uku a manyan masu tallafawa na duniya. Ya bude wannan gidauniyar ne a 1981 da burin bunkasa bangaren lafiya, ilimi da tattalin arzikin mutane a duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel