Shehu Sani: An kara kama wani babban dan kasuwa a Kaduna

Shehu Sani: An kara kama wani babban dan kasuwa a Kaduna

Wasu mutane sanye da kakin sojoji sun yi awon gaba da wani dan kasuwa mai suna Alhaji Ibrahim Musa Gashash wanda aka fi sani da Sardaunan Matasa, daga gidansa dake Kakuri.

Mutanen sun kai 20 kuma sun isa gidansa ne wajen karfe 3 na yammacin yau Laraba. Sun bukaci dan kasuwar dake bacci da ya fito waje.

An gano cewa, duk da gidan dan kasuwar yana kasancewa da abokan harkokinsa, yayi biyayya inda ya bi su har bayan motar da suka zo da ita.

Kamar yadda wani makusancin iyalan ya bayyana, yace da shi kadai sojojin suka tafi kuma basu bada kwakwaran dalilinsu na yin hakan ba.

DUBA WANNAN: Tura ta kai bango: Fafaroma ya buge hannun wata mata da ta makalkale shi don kauna

“Bai yi wani musu ba saboda mutanen dauke suke da manyan makamai. Amma har yanzu babu wata cibiya ko runduna ta ‘yan sanda da suka tuntubi iyalansa a kan kamen,” in ji shi.

Neman da wakilin jaridar Daily Trust yayi don gano wanne bariki aka kai shi, amma har yanzu babu nasara. Domin duk inda aka tuntuba sun musanta sanin abinda ya faru.

Wakilin jaridar Daily Trust ya kai ziyara gidan dan kasuwan dake Kakuri wajen karfe 3:50 na yamma, amma an ga gidan ba mutane sosai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel