Tirkashi: An dakatar da daurin aure a Jigawa bayan an gano cewa angon yana dauke da cutar kanjamau

Tirkashi: An dakatar da daurin aure a Jigawa bayan an gano cewa angon yana dauke da cutar kanjamau

- Wata amarya wacce kwananta bai kare ba ta tsallaka rijiya da baya a jihar Jigawa

- A wajen daurin aure ne aka gwada ango aka gano yana dauke da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV

- Wannan ya kasance tamkar mabudin ido ga masu yunkurin aure wajen yin gwajin cutukan jini

Wani daurin aure ya tarwatse a jihar Jigawa a cikin ranakun karshen makon da ya gabata.

Ba a gida lamarin ya fasu ba, sai a wajen daurin auren bayan da jama'a suka taru don kulla auren.

Wannan lamarin ya auku ne bayan da aka yi wa Ango gwajin kanjamau kuma aka same shi da cutar a jiki.

Wani ma'aboci amfani da kafar sada zumuntar tuwita mai suna Ussy, ya bayyana yadda aka gwada angon a wajen daurin auren kuma aka gano yana dauke da cuta mai karya garkuwar jiki.

Wannan lamarin kuwa ya jawo cece-kuce daga ma'abota amfani da kafafen sada zumuntar zamani ta tuwita.

KU KARANTA: Dan Allah ku dinga sanya mu a hanya idan munyi abinda ba daidai ba - Sanata Ahmad Lawan ya roki 'yan Najeriya

Kamar yadda Ussy yace: "An fasa daurin aure a jihar Jigawa bayan da aka gwada ango a wajen daurin aure aka gano yana dauke da cuta mai karya garkuwar jiki. A hakan ne kuwa 'yan daurin aure suka tafi da alawa da aka rarraba tare da goro. Wannan amarya ya kamata ayi mata sam barka saboda ta tsallake rijiya da baya."

A tsokacin da Zulai Umar tayi a tuwita, "wannan ya kamata ya kasance darasi ga 'yan baya. A dage da gwajin cutukan dake cikin jini kafin a kai ga maganar aure."

Shi kuwa Zannah cewa yayi, "wannan ganganci ne. Kafin a kai ga tara jama'a balle a kai ga asarar kudi ne ya kamata ayi wannan abun kunyar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel