Tinubu ya gana da Atiku da gwamna Fintiri

Tinubu ya gana da Atiku da gwamna Fintiri

- Tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigo a jam'iyyar APC, Ahmed Bola Tinubu, ya gana da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar

- Shuwagabannin sun shiga nishadi a lokacin da suka yi gaishe-gaishe tare da hira a haduwar da suka yi a Minna, jihar Neja

- Tinubu ya je Minna ne don karbar digirin girmamawa daga jami'ar Badamosi Babangida da ke Lapai a jihar Minna

Tsohon gwamnan jihar Legas kuma shugaban jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu a ranar Asabar ya hadu da tsohon mataimakin shugaban Kasa, Atiku Abubakar.

Atiku Abubakar shi ne dan takarar jam'iyyar PPP a zaben 2019 na shugabancin kasa.

Shuwagabannin sun shiga nishadi a lokacin da suka yi gaishe-gaishe tare da hira a haduwar da suka yi a Minna, jihar Neja.

DUBA WANNAN: Har ila yau: Jerin wasu kadarorin tsohon gwamna Kalu da EFCC zata kwace bayan an tura shi kurkuku

An gano cewa, Tinubu ya je Minna ne don karbar digirin girmamawa daga jami'ar Badamosi Babangida da ke Lapai a jihar Minna.

Hakazalika, Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri na tare da Atiku Abubakar inda Gwamna Sani Bello na jihar Neja ya tari Tinubu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel