Jiga-jigan 'yan majalisar tarayya 9 na APC da suka sha kaye a kotun daukaka kara

Jiga-jigan 'yan majalisar tarayya 9 na APC da suka sha kaye a kotun daukaka kara

Zaben Najeriya na 2019 ya kammalu kuma an sanar da wadanda suka yi nasara, amma kotun daukaka kara har yanzu tana jin kararraki daga jama’a wadanda basu gamsu da zaben ba. Wasu daga cikin wadanda hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta bayyana a matsayin masu nasara, kotun ta kan kwace ko kuma ta jaddada.

A wannan rubutun da Legit.ng ta yi, ta tattaro wasu jiga-jigan Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai karkashin jam’iyyar APC da suka sha mugun kaye a kotun daukaka karar.

1. Abdulmumin Jibrin, mazabar tarayya ta Kiru/Bebeji, Kano

An kwace kujerar dan majalisar ne a ranar Juma’a 1 ga watan Nuwamba, kuma kotun daukaka karar ta bada umarnin sake zabe a yankin a cikin kwwanaki 90. Aliyu Datti Yako, dan takarar kujerar karkashin jam’iyyar PDP ne ya kalubalanci nasararsa.

2. Alhaji Bala Hassan, mazabar tarayya ta Sokoto ta Arewa da Sokoto ta Kudu, jihar Sokoto

Dan takarar kujerarsa karkashin jam’iyyar PDP, Abubakar Abdullahi ne ya kalubalanci nasarasa. Kotun daukaka karar ta bukaci a yi sabon zabe a cikin kwanaki 90 bayan yanke hukuncinta.

3. Mohammed Lawal, mazabar tarayya ta Ajaokuta, jihar Kogi

Aloysius Okino, dan takarar jam’iyyar PDP ne ya kalubalanci nasarar Lawal. Kotun daukaka karar ta bukaci INEC da ta sauya zaben a akwatuna 21 na yankin.

4.Albert Akintoye, mazabar tarayya ta Okitipupa/Irele, jihar Ondo

A wannan akwai banbanci kadan. Dan takarar PDP din, Hon. Ikengboju Gbenga ne ya lashe zabe kamar yadda INEC ta bayyana. Amma kotun sauraron kararrakin zabe sai ta kwace kujerar ta ba Akintoye, a kan cewa Gbenga na da shaidar zama dan wata kasa amma a Najeriya aka haifesa.

Daga baya sai kotun daukaka kara ta maidawa Gbenga kujerar a kan cewa, asalin mahaifarsa Najeriya ce. Samun shaidar zama dan wata kasa ba hujja bace.

DUBA WANNAN: Rusau: KASUPDA ta rushe gidaje 300 a Kaduna

5. Sanata Abubakar Tambuwal, mazabar Sokoto ta Kudu

Kotun daukaka kara ta kwace kujerar Tambuwal tare da umartar dan takarar PDP, Ibrahim Danbaba da ya maye gurbinsa.

6. Aliyu Shehu, mazabar tarayya ta Bodinga/Dange Shuni/Tureta, jihar Sokoto.

Kotun daukaka kara ta soke nasararsa tare da umartar Balarabe Kakale na jam’iyyar PDP ya maye gurbinsa.

7. Alhassan Doguwa, mazabar tarayya ta Tudunwada/Doguwa, jihar Kano

Kotun daukaka kara ta soke nasararsa duk da yana shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai. Yusha’u Salisu na jam’iyyar PDP ne ya kalubalanci nasararsa. Kotun ta bukaci a sake sabon zabe a yankin.

8. Emmanuel Uduaghan, tsohon gwamnan jihar Delta kuma sanata mai wakiltar Delta ta Kudu

Kotun daukaka kara ta bayyana Manaja a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar, ta soke hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe tare da bada umarnin yin sabon zabe.

9. Sanata Adedayo Adeyeye, Ekiti ta Kudu,

A hukuncin da ya ba kowa mamaki, kotun daukaka kara ta kwace kujerar mai magana da yawun majalisar dattawan Najeriya, Adedayo Adeyeye. Ta mika kujerar ga Sanata Biodun Olujimi ta jam’iyyar PDP a matsayin wacce ta yi nasarar lashe zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel