Mahaifina sai yayi zina dani a kowanne zangon karatu kafin ya biya min kudin makaranta

Mahaifina sai yayi zina dani a kowanne zangon karatu kafin ya biya min kudin makaranta

- Wata matashiya mai shekaru 20 a duniya ta bayyana yadda mahaifinta kuma babban fasto ya fara kwanciya da ita tun tana da shekaru 13

- An cafke mahaifinnata tare da wasu masu irin halinshi har guda biyar akan laifin kwanciya da ‘yan uwansu ko kuma keta haddi

- A cikinsu akwai wani fasto mai shekaru 33 da ya yi wa ‘yarshi mai shekaru 10 a duniya fyade bayan da aka bar shi da ita a gida

Yarinyar mai suna Fortune, matashiya mai shekaru 20, ta yi wa jami’an ‘yan sanda bayanin yadda mahaifinta ya fara kwanciya da ita tun tana da shekaru 13 a duniya. Haka zalika, mahaifinnata yana bukatar ya kwanta da ita a kowanne zangon karatu kafin ya biya mata kudin makaranta.

Mahaifinnata shine babban fasto na majami’ar Mount Zion Light House Full Gospel, dake layin Obio Imo, cikin karamar hukumar Uyo dake jihar Akwa Ibom. Hukumar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom ta cafke faston Williams Okon Bassey.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar, Odiko MacDon, ya bayyana cewa, an cafke wasu mutane shida har da faston a kan zargin kwanciya da ‘yan uwansu tare da keta musu haddi. Ya sanarwa da kamfanin dillancin labarai yadda Fortune ta labarta musu sau uku mahaifinnata na dirka mata ciki.

KU KARANTA: Yadda wani furodusa ya nemi yayi zina dani na tsawon sati daya kafin ya sanya ni a wani sabon fim - In ji wata fitacciyar jaruma

Ya kara da cewa: “Matashiyar ta ce, mahaifinta ya fara kwanciya da ita tun tana da shekaru 13 a duniya, saboda yawan lalata da yake da ita ne yasa ta dauki ciki har sau uku, wanda mahaifiyarta ta zubar mata.

“Ta cigaba da bayyana cewa, lokaci na farko da mahaifinata ya fara keta mata haddi, shine a cikin dakin shiryawarshi da ke cikin cocin. Ya yi barazanar tsine mata matukar ta fallasa sirrin su. Yana kuma bukatar kwanciyar da ita kafin ya biya mata kudin makarantarta ko wasu bukatu nata.”

Haka kuma idan ba a manta ba a ranar 13 ga watan Oktoba, an kama wani fasto mai suna Awanga Essien Udo, mai shekaru 33 a duniya da laifin lalata da ‘yarshi mai shekaru 10 a duniya.

Mai Magana da yawun ‘yan sandan, ya ja kunnen masu irin wannan bakin halin akan su kiyaye kafin su hadu da fushin hukuma. Ya kara da shawartar iyaye dasu hanzarta kai wa jami’an tsaro rahoton ire-iren wadannan lamurran.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel