Dansanda ya harbi wani mutumi saboda ya auri budurwar da abokinsa yake so

Dansanda ya harbi wani mutumi saboda ya auri budurwar da abokinsa yake so

Wani mutumi mai aikin wanki da guga a jahar Legas, Blessing Demian yana neman agaji tare da namen kai masa dauki bayan wani dansanda ya dirka masa harsashi a kafarsa kawai saboda yana soyayya da budurwar abokin Dansandan.

Jarida Punch ta ruwaito Demian ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a da misalin karfe 9:45 na dare a unguwar Oke0Afa, Isolo na jahar Legas a ranar 14 ga watan Satumba yayin da yake dawowa daga shagonsa.

KU KARANTA: Yansandan SARS sun kama wani mutumi saboda ya ajiye gemu, beli N50,000

A cewarsa, yana hanyarsa ta komawa gida kenan sai wani dansanda mai suna Kenneth Kadire dake aiki a ofishin Yansanda na Ejigbo ya dirka masa bindiga a kafarsa ta dama kawai saboda ya yi soyayya da budurwar abokin Dansandan, har ma ya aureta.

Ita dai wannan mata da aka yi wannan harbi saboda ita ta taba soyayya da abokin Dansanda Kenneth, amma daga bisani suka rabu, ta koma wajen Demian mai wanki da guga, har ta kai ga sun yi aure, ashe hakan bai ma Kenneth mai fushi da fushin wani, dadi ba.

“Ina kan hanyar komawa gida daga wajen aiki a kan babur dina sai aka tsayar dani a wani shingen binciken ababen hawa na Yansanda, na tambayeshi ko lafiya? Sai yace wai bani da hankali, kafin na ankara ya fara dukana, sai matata ta sauka daga kan babur tana bashi baki, nan ma ya shiga dukanta.

“Kafin ka ce me, ya ingiza ni cikin motar Yansanda yace wai ni dan fashi ne, kawai sai ya dirka min bindiga a kafa, har ya yi barazanar halakani da matata tare da jefar da gawarwakinmu. Nan ya cigaba da cewa kamata yayi bayan na auri matata na mayar da kudin da abokinsa ya kashe mata a lokacin da suke soyayya, amma tunda bamu biya ba, zamu biya da rayuwarmu. A garin harbina ma sai da ya samu wasu mutane biyu.” Inji shi.

Da aka tuntubi rundunar Yansandan jahar, kaakakinta, Bala Elkana ya tabbatar da lamarin, sai dai yace bayan aukuwar lamarin DPO na Yansandan Ejigbo ya kula da Demian ta hanyar biyan kudin asibitinsa, kuma sun yi alkawarin hukunta Dansanda Kenneth, amma yace a ba laifin rundunar Yansanda bane.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel