Sojoji sun tarwatsa sansanin yan bindga guda 2 a jahar Kaduna

Sojoji sun tarwatsa sansanin yan bindga guda 2 a jahar Kaduna

Hadakan dakarun rundunar Sojin Najeriya na Operation Thunder Strike, rundunar Operation Whirl Punch da kuma rundunar atilary ta 312 sun tartwatsa wasu sansanonin miyagu yan bindiga a jahar Kaduna.

Rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN, ta bayyana cewa kaakakin runduna ta 1 na Sojan Najeriya, Kanal Ezindu Idimah ne ya bayyana haka inda yace Sojojin sun kai wannan samame ne da misalin karfe 2 zuwa 4 na daren Lahadi.

KU KARANTA: Ku rage farashin sayen Data – Minista Pantami ga kamfanonin sadarwa

“Mun kai wannan hari ne da nufin kakkabe ragowar yan bindiga a jahar Kaduna tare da lalata sansanoninsu a Kankomi dake kusa da tsaunukan Tantu da Daban Goje cikin karamar hukumar Chikun na jahar.

“A yayin samamen Sojoji sun lalata sansanoni guda biyu da yan bindigan suke amfani dasu wajen shirya muggan ayyuka, haka nan Sojoji sun kashe dan bindiga 1, sun kwato bindigar AK 47 1, babura 3, wayoyin salula 2 da N5000.” Inji shi.

Daga karshe Ezindu Idimah yace wannan ne karo na hudu cikin kwanaki 10 da Sojoji suke samun nasara a kan yan bindiga wanda hakan ke kaisu ga kwato tarin makamai da kuma ceto mutanen da aka yi garkuwa dasu.

A wani labari kuma, jam’iyyar adawa ta PDP reshen jahar Kogi ta gargadi gwamnan jahar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufa’i da kada ya kuskura ya taka kafarsa a jahar a yayin gudanar da zaben gwamnan jahar.

Kaakakin jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa dya fitar, inda ya yi kira ga El-Rufai daya shawarci Gwamna Yahaya Bello ya dauki dangana da kayin da zai sha saboda PDP ce za ta lashe zaben 16 ga watan Nuwamba, a cewarsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel