Tirkashi: Wani mutum mai 'ya'ya 100 ya auro mata 4 don bukatar karin haihuwa

Tirkashi: Wani mutum mai 'ya'ya 100 ya auro mata 4 don bukatar karin haihuwa

- Wani mutum dan shekaru 94 a kasar Uganda ya auri mata 4 a lokaci daya don bukatar karin haihuwa

- Ba auren mata 4 ne abin mamaki ba, sai ikirarin da yayi na son karin haihuwa duba da yana da yara 100 a duniya

- Ssemakula ya ce, mata da yara su ke bashi nishadi kuma sune sirrin arzikinsa

Wani mutum dan kasar Uganda mai yara 100 ya karo mata hudu sakamakon Karin bukatar haihuwa da yake.

Nulu Ssemakula mai shekaru 94 a duniya mazaunin kauyen Ruyonza ya kara fadada iyalansa.

Ssemakula musulmi ne wanda ya sake farali a shekara 1977 kamar yadda jaridar Ugandan Monitor ta ruwaito.

KU KARANTA: Tsoffin soji masu murabus sun bukaci gwamnatin tarayya da ta kafa musu ma'aikatarsu

Ssemakula wanda ya yi nasarar fadad iyalinsa na da mata sama da 19 wadanda suka Haifa masa yara 100 kuma a halin yanzu yana bukatar kari. Karamin dansa yana da watannni 10 a duniya kuma amaryarasa mai shekaru 24 na da cikin wani dan.

A halin yanzu yana tare da ‘ya’yansa 66 kanana. A yayin da awasu daga cikin yaransa suka haifa masa jikoki, kakan y ace shi kuwa yana bukatar Karin haihuwa, a don haka ne ya karo mata 4.

Ssemakula ya auri matarsa ta farko ne a shekarar 1952 wacce bata dade bay a karo mata abokan zama 5.

“Matana 4 suka rasu a gidana, wasu kuma da suka nuna bazasu iya zama dani ba sun tafi sun barani da yara. Zan kuma kara auro wasu matan in har ina da sauran kwana. A wajen mata da yarana nake samun nishadi. Su ne gaskiyar arzikina.” in ji Ssemakula.

A halin yanzu, Ssemakula ya gina masallaci da makarantar firamare da kuma in jin tatsar nonon shanu don kula da iyalinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel