Yadda na zama hamshakin mai arziki a shekaru 25, in ji wani gwamna

Yadda na zama hamshakin mai arziki a shekaru 25, in ji wani gwamna

- Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya bayyana cewa, ya zama biloniya tun yana da shekaru 25 a duniya sakamakon jajircewarsa

- Gwamnan y ace, yayi aiki tukuru sannan kuma shi hamshakin mai arziki ne

- Gwamnan ya sanar da 'yan kasuwar Abakpa cewa na dage ranar komawarsu babbar kasuwar jihar zuwa ranar 10 ga watan Janairu, 2020

Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya ce, ya zama hamshakin mai arziki ne tun yana da shekaru 25 kacal a duniya sakamakon jajircewarsa da aiki tukuru.

Umahi wanda yayi wannan jawabin ga shuwagabannin kasuwar Abakpa da ke Abakaliki, ya karayata rahoton shafukan sada zumunta cewa ya na da shago a kasuwar kuma ya gina gidansa cikin shekara daya, kamfanin dillancin labarai ya ruwaito.

KU KARANTA: Majalisar jihar Legas ta yi barazanar kama tsohon gwamnan jihar

Jaridar Legit.ng ta gano cewa, gwamnan yace, “Na dage nayi aiki tukuru; nib a matalauci bane, ni hamshakin mai kudi ne. Bani da shago a kasuwar nan kuma banda ra’ayin hakan.”

Ya sanar da cewa za a canza sunan kasuwar daga kasuwar Abakpa zuwa kasuwar kayan marmari da kayan gwari ta Ebonyi.

A halin yanzu muna da mataimaki na musamman akan lamurran kasuwanni; za a gyara gine-ginen kasuwar. ‘Yan kasuwar na da zabi biyu: Ko ku hyara gininya zama naku ko kuma gwamnati ta gyara ya zama mallakinta.” in ji gwamnan.

Ya sanar da ‘yan kasuwan cewa, saboda sa bakin da kungiyar kiristoci ta kasa tayi, an dage komawarsu babbar kasuwar jihaqr zuwa 10 ga watan Janairu, 2020.

Ya kara da bada umarnin cewa, shagunan da aka rufe kwanaki aka kuma budesu, a kara rufesu saboda ‘yan kasuwar sun ki janye karar gwamnatin jihar da suka kai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel