Jerin sunayen sojin najeriya 22 da suka tsere daga fagen fama

Jerin sunayen sojin najeriya 22 da suka tsere daga fagen fama

- Rundunar sojin Najeriya na neman wani manjo da yaransa 21 da suka tsere daga bakin daga a jihar Barno

- Ana zargin sojojin 22 sun gudu ne a harin da 'yan ta'addan Boko Haram suka kai garin Gubio na jihar Barno

- Manjon da yaransa sun bace ba amo ba labari, a don haka ne rundunar sojin ke nemansu don fuskantar hukuncin laifukansu

Rundunar sojin Najeriya na zargin wani manjo da soji 21 da tserewa daga filin dagar yaki da Boko Haram. A don haka ne ake nemansu ido rufe, inji majiya daga rundunar sojin.

Sojin zasu fuskanci hukuncin abinda suka yi idan aka kamasu saboda babban laifi ne tserewa daga bakin gama.

An ce sojin sun gudu ne yayin da Boko Haram suka kai hari Gubio, wani yankin jihar Barno da 'yan ta'addan suka kwace a ranar 29 ga watan Satumba.

Rahoto daga jaridar Premium times ya nuna cewa, an kashe sojoji 18 yayin harin.

Rundunar sojin Najeriya basu tabbatar da yawan wadanda aka kashe ba amma manyan sojin sun hanzarta fara bincike don gano yawan illar da aka musu.

Daga baya sai suka gano cewa babu sojoji 21 kuma babu wata shaida da ta nuna 'yan ta'addan ne suka yi awon gaba dasu.

KU KARANTA: Jarumin maza: Ya bige masu garkuwa da mutane tare da sakin mutane da suka kama

Babu tabbacin cewa zargin guduwar manjon da yaransa na da nasaba da jan kunne daga shugaban sojin, Tukur Buratai, inda ya hani sojojin barin inda aka ajesu yayin harin 'yan ta'addan.

Buratai ya maimaita jan kunnen a watan Yuni inda ya zargi wasu sojojin da ragwanta wanda hakan ne yasa aka yi shekaru 10 ana yaki da ta'addanci.

Babu tabbacin yawan sojojin da ke tsare da Gubio da misalin karfe 4:30 na yamma, lokacin da 'yan ta'addan suka kai farmaki. Amma majiya daga rundunar ta ce an gano sojoji 22 da suka tsere.

Jerin sunayen sojojin da hukumar ta bayyana tana nemansu kamar yadda jaridar Premium times ta wallafa su ne: U. A Nagogo, mai mukamin manjo, Malam Turaki, mai mukamin sajan, Sajan Benjamin Afolabi, Sajan Christian Nwachukwu, Sajan Patrick Kosin, Sajan Amuwa Orin, Sajan Ibrahim Amodu, Sajan Nasiru Umar, Sajan Bello Suleiman, Sajan Josiah Seth da Sajan Muazu Nura.

Sauran sun hada da: Kofur Ayodeji Ogunsuji, Kofur Michael Friday, Kofur Wakili Saul, Kofur Akyen Zamani, Kofur Yahaya Abubakar Doia, Kofur Isikuru Venture, Kofur Aminu Ishiaku, Kofur Usman Suleiman, Kofur Maigari Markus, Kofur Edward Ofem da Kofur Adams Shehu.

Ana zargin su da barin aikinsu tare da tserewa zuwa inda ba a sani ba. A don haka za a kamasu in har aka gansu tare da basu hukuncin da ya dace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel