Jirgin yakin Najeriya ya cilla bama bamai a motocin yakin Boko Haram

Jirgin yakin Najeriya ya cilla bama bamai a motocin yakin Boko Haram

Dakarun rundunar Sojan sama sun tafka ma kungiyar mayakan Boko Haram mummunan ta’asa ta hanyar amfani da jiragen yaki wajen sauke musu ruwan bama bamai a kan wasu manyan motocin yakin yan ta’adda.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin rundunar Sojan sama, Ibikunle Daramola ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Laraba a babban birnin tarayya Abuja, inda yace gaba daya motocin sun tashi aiki.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta cika hannu da yan Yahoo-yahoo 13, ta kama manyan motoci 5

A cewar Daramola, jirgin Alpha Jet mallakin rundunar Sojan saman ne ya fara zuwa shawagi a sararin samaniyar yankin Gudumbali-Zar-Garunda inda ya gano dandazon yan ta’adda a yankin Jumaacheri sun nufi Garunda.

“Yan ta’addan sun yi kokarin bacewa, amma jirgin ya gano inda suke ya cigaba da bibiyansu, a daidai lokacin ne jirgin yakin ya fara sauke musu ruwan bamabamai tare da lalata motocin duka, tare da kashe dukkanin yan bindigan dake wurin, da bisani motocin sun yi ta fashewa sakamakon tarin makaman dake cikin motocin suna fashewa.” Inji shi.

Daga karshe kaakaki Daramola ya bayyana cewa za su cigaba da kokarin kakkabe ragowar yan bindiga dake yankin Arewa maso gabas.

A wani labara kuma, akalla mutane uku ne suka rasa ransu yayin da mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram suka kai wani samame garin Nganzai dake cikin jahar Borno a ranar Litinin, 9 ga watan Satumba.

Wani shaidan gani da ido, kuma dan banga a yankin daya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace yan bindigan sun kai harin ne da misalin karfe 9 na dare, inda suka afka kauyen Mallam Kaleri dake kusa da Gajiganna a garin Nganzai.

Baya ga mutane uku da yan ta’addan suka kashe, dan bangan yace sun ji ma wasu mata biyu rauni sa’ilin da suka bude ma mazauna garin wuta a daidai lokacin da suka afka cikin kauyen.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel