Buhari ya nadawa hukumar NDLEA sabon sakatare

Buhari ya nadawa hukumar NDLEA sabon sakatare

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Shadrach Haruna a matsayin sabon sakataren hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya wato National Drug Law Enforcement Agency (NDLEA).

Kakakin hukumar NDLEA, John Achema ne ya fitar da wannan labarin ranar Litinin a Abuja, inda ya ce sabon sakataren zai maye gurbin Roli George ne wanda wa’adinsa ya kare a watan Yunin 2018.

KU KARANTA:Buhari ya bada umarnin kwaso ‘yan Najeriya daga kasar Afirka ta Kudu

A cewar Mista Achema aikin sakataren hukumar shi ne kula da duk wadansu muhimman takardun da suka shafi ayyuka da kuduroran hukumar NDLEA.

“Wannan nadin zai fara aiki ne kai tsaye”, inji Kakakin. Achema ya kara da cewa Haruna kwararren lauyane wanda ya jima yana aiki da ma’aikatar shari’a ta Najeriya.

Haka zalika, ya yi aiki har a kasashen waje, inda yake aiki a wata ma’aikatar shari’a mai kula da muggan laifuka ta sakatariyar Commonwealth dake birnin Landan.

Kamfanin dillacin labaran Najeriya wato NAN ne ya fito mana da wannan labarin.

A wani labarin mai kama da wannan kuwa zaku ji cewa, Shugaba Buhari ya bada umarnin a kwaso ‘yan Najeriya daga kasar Afirka ta Kudu zuwa gida Najeriya.

Shugaban kasan ya bada wannan umarnin jim kadan bayan da ya tarbi tawagar da ya aikawa shugaban kasan Afirka ta Kudu wato Cyril Ramaphosa. Buhari ya bai wa ministan harkokin kasashen wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama umarnin cewa a kwaso ‘yan Najeriya cikin gaggawa domin maido da su gida.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel