Akwai 'yan Boko Haram a kowacce kabila ta kasar nan - Gwamnan Borno

Akwai 'yan Boko Haram a kowacce kabila ta kasar nan - Gwamnan Borno

- Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya bayyana cewa akwai 'yan Boko Haram a kowacce kabila dake kasar nan

- Gwamnan ya bayyana hakan ga manema labarai jim kadan bayan kammala ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa dake Abuja

- Gwamnan ya bayyana cewa ya ziyarci shugaban kasar ne domin yi masa bayani akan harin da aka kai kananan hukumomin Gubio da Magumeri

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya bayyana cewa 'yan kungiyar Boko Haram suna cikin kowacce kabila ta kasar nan.

Gwamnan yayi wannan magana ne a lokacin da ya gana da manema labarai jim kadan bayan kammala ganawar da yayi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa dake babban birnin tarayya Abuja.

Domin kawo karshen ta'addancin a jiharsa da ma yankin arewa maso gabas baki daya, gwamnan yayi kira da a dauki mataki na gaggawa domin kawo karshen lamarin da yake ta kara yaduwa a kasar nan.

KU KARANTA: Hotuna: Yadda sojojin saman Najeriya suka kera sabon jirgin sama mai saukar Ungulu

Sannan gwamnan ya nemi da a kara tura jami'an tsaro musamman zuwa garuruwan da abin yafi karfi a jihar ta shi.

Ya ce: "Babbar matsalar da muke da ita a jihar Borno shine mun hada iyaka da kasashe har guda uku, jamhuriyar Nijar, kasar Chadi, da kuma kasar Kamaru."

A cewarsa ya ziyarci shugaban kasar ne domin yayi masa bayani akan harin da aka kai kananan hukumomin Gubio da Magumeri da kuma wasu kananan matsaloli.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel