Rundunar 'yan sanda ta yi bajakolin wasu 'yan luwadi a jihar Sokoto (Hoto)

Rundunar 'yan sanda ta yi bajakolin wasu 'yan luwadi a jihar Sokoto (Hoto)

Kwamishinan 'yan sandan jihar Sokoto, CP Ibrahim Kaoje, ya bawa iyaye shawarar cewa su ke samun lokaci su na zama da 'ya'yansu kananu domin yi musu tambayoyi a kan irin mutanen da su ke mu'amala da su a waje.

CP Kaoje ya bayyana hakan ne yayin bajakolin wasu masu laifi su 7, da suka kware a fashi da makami, fyade, tu'ammali da miyagun kwayoyi da kuma luwadi.

A cewar Kwamishinan, jami'an 'yan sanda sun kama wani mutum, Shamsuddeen Muhammad, da ke zaune a karamar hukumar Kware, da wata bakar leda da ke cike da tabar wiwi, kwayar D5 guda 300 da kuma kuma kwayar Exol 5 guda 175.

Kazalika, ya bayyana cewa sun kama Bello Yusuf mazaunin karamar hukumar Wurno da Nafiu Abubakar mazaunin yankin Kwanawa a garin Sokoto, da kwayoyin D5 175, kwayar Exol 5 guda 941, wayar sata da kullin tabar wiwi 52.

Da ya ke gabatar da Shehu Amadu, mai shekaru 21, da Muzambilu Muhammad da Shafiu Almustapha, bisa zarginsu da aikata luwadi, CP Kaoje ya yi kira ga shugabannin addini da su ke fadakar da jama'a a kan illolin da ke cikin luwadi.

DUBA WANNAN: Matasa sun fara atisayen tsaftace mahaukata da ke gararamba a titunan garin Kaduna

Kwamishinan ya bayyana fyade da luwadi a matsayin manyan matsaloli da ke addabar al'ummar wannan zamani.

An kama Muhammad da Almustapha bayan 'yan sanda sun samu rahoton cewa sun kulla mu'amalar luwadi a tsakaninsu, wanda yin hakan ya saba wa dokar Najeriya.

Rundunar 'yan sanda ta yi bajakolin wasu luwadi a jihar Sokoto (Hoto)
Rundunar 'yan sanda ta yi bajakolin wasu luwadi a jihar Sokoto
Asali: Facebook

Da ya ke magana da manema labarai, daya daga cikin wadanda ake zargi, Almustapha, ya amsa laifinsa tare da bayyana ya shiga harkar luwadi ne shekaru shida da suka gabata.

"Tun ina karami wani mutum a unguwarmu ya fara luwadi da ni. Sai ya kira ni gidansa ya bani kudi don ya kwanta da ni.

"Ni ma da na fara girma, sai na samo wanda za mu ke yin luwadi tare, duk lokacin da mu ke so.

"Mun fi shekara shida mu na mu'amala. Ina kiransa a waya duk lokacin da na ke bukatarsa, ko kuma na je shagonsa ko gida mu yi abinda muke so.

"Ni ne miji, shi kuma Muhammad mata ta. Si ma wasu lokutan na kira na idan yana bukata ta," a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Za ka iya aiko mana da labari ta hanyar cike wanna fom da ke kasa:

https://docs.google.com/forms/d/e/1FAIpQLSch6m8qBDJY3fmT8OH0Dy7Sqkrvwt-tveaPURetOsKjYb_4cQ/viewform

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel