Babbar magana: Dan Allah ku taimaka mini ina neman mijin aure na gari amma mai kudi - In ji wata budurwa

Babbar magana: Dan Allah ku taimaka mini ina neman mijin aure na gari amma mai kudi - In ji wata budurwa

- Wata budurwa ta nemi Hausawa su taimaka su nema mata mijin aure amma fa mai kudi

- Budurwar ta dauki kanta a wani bidiyo inda take hada mutane da Allah da Annabi akan su taimaka mata da mijin aure na gari amma fa mai kudi

- Ta ce ta gaji da zaman gwaurancin da take yi saboda da yawa daga cikin kawayenta duk sunyi aure

Wani bidiyo da ya dinga yawo a shafukan sada zumunta, ya nuna yadda wata budurwa ta zage tana rokon Hausawa akan a taimaka a nema mata mijin aure na gari amma fa mai kudu.

Buduruwar da ta dauki bidiyon ba ta bayyana sunanta ba, amma ta bayyana cewa tayi irin wannan bidiyo cikin harshen Faransanci ba ta dace ba, shine yasa ta koma yi da harshen Hausa ko Allah zai sa ta dace.

KU KARANTA: Allah ya kyauta: 'Yan daukar amarya sun kashe wani yaro a wajen neman abincin shi a jihar Kano

Ga abinda budurwar ta ce:

"Ku nemo min miji na gari, na roke ku dan girman Allah, dan darajar Manzon Allah (SAW) ku taimaka ku nemo min miji na gari mai kudi sosai.

"Na yi wannan bayani da yaren Faransanci, amma ban dace ba, shine nace bari nayi da yaren Hausa ko zan dace, saboda wallahi na gaji da zaman gwaurancin da nake yi.

"Duk abokaina sunyi aure, wasu daga cikinsu ma an sake su amma sun sake yin wani auren ni kuma ko daya banyi ba.

"Dan Allah jama'a ko auren wata daya ne ina so, ni kawai ina so naji yadda ake ji idan anyi aure."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel