Kwamishinan 'yan sandan Taraba ya bada gonarsa kyauta domin a gina makabarta

Kwamishinan 'yan sandan Taraba ya bada gonarsa kyauta domin a gina makabarta

- Kwamishinan 'yan sandan jihar Taraba, CP Sanusi Alkasim ya bayar da katafariyar gonarsa domin gina makabarta

- Gonar dai na a garinsa ta Sandamu da ke Karamar Hukumar Sandamu ta Jihar Katsina

- Ya sadaukar da wannan gona ne da ke jikin makaartar garinsu domin a fadada makwancin mamata

Rahotanni sun kawo cewa Kwamishinan 'yan sandan jihar Taraba, CP Sanusi Alkasim ya bayar da katafariyar gonarsa da ke jikin makababartar garinsu wato Sandamu da ke Karamar Hukumar Sandamu ta Jihar Katsina kyauta domin ingantawa da fadada makwancin a'lumma bayan rasuwarsu.

Majiyarmu ta kawo cewa CP Alkasim ya yi kyautar katafariyar gonar tasa duk da cewa a cikin gari take, sannan kuma gine-gine sun yawaita a yankin.

Kamar yadda aka sani hakan na daga cikin sadakar da ake yiwa lakabi da sadakatin jariya, wanda mutum zai ci gaba da kwasar lada daga wajen mahaliccinsa koda bayan babu ransa.

KU KARANTA KUMA: To fah: Cin mutuncin Naira babban ta'addanci ne - Babban Banki

A wani labari na daban, Legit.ng ta kawo cewa wasu mutane biyu da majiyar mu ba ta san sunayensu ba sun mutu sakamakon jan su da wutar lantarki ta yi yayin da suke gyaran fitilar haskaka titin NNPC a garin Kaduna.

Majiyar mu ta sanar da mu cewa mutanen biyu sun gamu da ajalinsu bayan sun yi amfani da tsani na karfe domin gyaran fitilar.

Mutanen biyu; wanda ya hau tsanin da wanda ya rike, duk sun mutu sakamakon jan su da wutar lantarki ta yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel