Al'ada kowa ta irin ta sa: Dalilin da yasa mata masu dukiya ke auren mata 'yan uwansu a kasar Tanzania

Al'ada kowa ta irin ta sa: Dalilin da yasa mata masu dukiya ke auren mata 'yan uwansu a kasar Tanzania

A yankin Musoma na kasar Tanzania, mace mai dukiya (yawan shanu) da ba ta da miji ko dan da zai kula da ita har ta kai shekarun tsufa, za ta iya auren mace budurwa. Ana kiran irin wannan al'ada da suna 'nyumba ntobhu'.

Wannan al'ada ta fi karfi a yammacin kasar Tanzania. Al'ada ce ta gargajiya ta auren jinsi guda. Ma'auratan kan kwanta a gado daya, su yi rayuwa tare da yin dukkan wani abu da ma'aurata ke yi amma banda mu'amalar da ta shafi saduwa (jima'i).

A yankin Mara, nyumba ntobhu na bawa dattijai mata damar auren 'yammata domin mallakar yaran matashiyar da suka aura da kuma taimaka musu wajen aiyukan gida. Mata sun bayyana cewa wanna al'ada na taimaka musu wajen kauce wa matsalar cin zarafinsu a cikin gidaje daga maza.

Kazalika, a'adar na bawa dattijai mata kariya daga zaman kadaici.

Wata dattijuwa. Mtongori Chacha, mai shekaru 57, wacce ta auri wata matashiya, Gati Buraya, mai shekaru 31, ta ce al'adar irin wannan aure ta samo asali ne sakamakon cin zarafin mata da maza ke yi a cikin rayuwar aure.

DUBA WANNAN: Yadda wata matashiya mai shekaru 14 ta hada baki da saurayinta suka kashe yayan ta

Chacha da Buraya na da yara uku. Chacha ta bayyana cewa ta yanke shawarar auren Buraya ne saboda ba ta samu haihuwa ba a auren da ta yi na farko da namiji, wanda ta ce ya sha cin zarafin ta.

Domin samun haihuwa a cikin irin wannan aure na mace da mace, ma'auratan kan dauko hayar namiji tare da biyansa kudi domin ya yi wa matashiyar matar ciki.

Ana kulla yarjejeniya da namijin da aka dauko haya a kan cewa ba zai yi ikirarin mallaka ko neman wani hakki a kan yaran da aka haifa ba.

Dattijuwar matar ce za ta dauki nauyin yaran da aka haifa kuma za su yi amfani da sunan ta a matsayin na mahaifi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel