Kamfanin siminti na Dangote ya sanya kaci-ci kaci-ci na biliyoyin kudi

Kamfanin siminti na Dangote ya sanya kaci-ci kaci-ci na biliyoyin kudi

-Kamfanin siminti na Dangote ya kaddamar da gasar kaci-ci kaci-ci da kwastomomi miliyan 21 za su amfana dashi.

-Kamfanin ya bayyana cewa an shirya gasar ne don a godewa kwastomonin kamfanin akan irin cinikayyar da suke yi ma kamfanin

-Haka zalika a gasar wadanda suka yi nasara zasu lashe kayayyaki da suka hada da motoci, babura, talabijin da dai sauransu

A ranar Alhamis 4 ga watan Yuli 2019, kamfanin siminti na Dangote ya kaddamar da gasar kaci-ci kaci-ci da kwastomominshi miliyan 21 za su amfana dashi.

Babban mai kula da sadarwa na kamfanin, Anthony Chiejina ne ya bayyana haka a lokacin da ake kaddamar da shirin a jihar Legas.

Chiejina ya ce “Mutane miliyan 21 ne za su yi nasara a wannan gasar da ba a taba yin irin ta ba a kasar nan.”

“Babbar gasa ce, kuma daidai take da fitar da kwatan yan Najeriya daga talauci.”

Ya bayyana cewa wannan gasar ta daban ce saboda an sanya ra’ayin da al’umma ke so kuma an shirya ta ne don a gode ma kwastomomin kamfanin akan irin cinikayyar da su keyi.

KARANTA WANNAN: Dalilin da ya sa muke so a raba auren mu bayan shekaru 27 - Ma'aurata

Haka zalika, babban daraktan kamfanin, Joseph Makoju ya bayyana cewa an shirya gasar da niyyar godewa kwastomomin kamfanin akan irin taimakon da suke ba kamfanin wanda hakan ya sanya yayi fice a fadin kasarnan.

Ya bayyana cewa za a gudanar da gasar ga kwastomomin masu siyan simintin 'Block Master', simintin '3X' da simintin 'Super Falcon'.

Haka zalika, daraktar kasuwanci ta kamfanin, ta bayyana cewa gasar za ta kara taimakawa wajen kawo ma kamfanin karin kudin shiga inda ta bayyana cewa za a saka katin gasar a buhunna miliyan 70.5 dauke da kyaututtuka daban daban.

Ta bayyana cewa za a gudanar da gasar daga ranar 1 ga watan Yuli 2019 zuwa 30 ga watan Satumba 2019. Ta bayyana cewa kyaututtukan sun hada da Motoci, babura, a dai daita sahu (Keke Napep), talabijin, kudade, katin waya da dai sauransu.

Ta bayyana cewa duk wanda ya kankare katin da ke cikin simintim kuma yayi nasara, to sai ya garzaya ofisoshin Dangote dake a yankuna da kuma wasu manyan wajajen da ake siyar da kayayyakin Dangote.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel