Yobe: Mirwa da Bello sun zama kakakin majalisa da mataimakinsa ba tare da adawa ba

Yobe: Mirwa da Bello sun zama kakakin majalisa da mataimakinsa ba tare da adawa ba

- Ahmed Lawan Mirwa da Auwalu Isah Bello sun zama kakakin majalisa da mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Yobe na bakwai

- Ishaiku Mohammed, magatakardar majalisar, ya gudanar da wani kira sannan ya tabbatar da hallaran mambobi majalisar dokokin 24 kafin a fara zaben

- Yan majalisar jihar sun zabi mambobin biyu bayan Buba Kalallawa, mai wakiltanyankin Damaturu ya gabatar da zabar su sannan takwarorinsa suka mara masa baya

Ahmed Lawan Mirwa da Auwalu Isah Bello sun zama kakakin majalisa da mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Yobe na bakwai a karkashin inuwar jam’yyar, All Progressive Congress (APC).

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sun zamo shugabannin majalisar biyo bayan lamunce masu da mambobin majalisar 24 suka yi.

Magatakardar majalisar, Ishaiku Mohammed, ya gudanar da wani kira sannan ya tabbatar da hallaran mambobi majalisar dokokin 24 kafin a fara zaben.

Buba Kalallawa, mai wakiltanyankin Damaturu ya gabatar da Ahmed Lawan Mirwa sannan mamba mai wakiltan Fika, Ishaku Audu ya mara masa baya.

KUKARANTA KUMA: Dino Melaye ya sha alwashin zama gwamnan Kogi a watan Nuwamba

Bayan yayi sanarwa sau uku ba tare da an amsa ba, magatakardar majalisar ya kaddamar da Mirwa a matsayin kakakin majalisar.

Haka zalika, Hon Bulama Bukar mai wakiltan ynkin Gujaba ya gabatar da Auwl Isa Bello, sannan Ahmed Mua Dumbulwa mai wailtan Yunusari ya mara masa baya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel