Bakar addu'a: Ya Allah ka kawowa mijina bakin talaucin da zai sa ya daina cin amanata a titi - Addu'ar wata mata ga mijinta kenan

Bakar addu'a: Ya Allah ka kawowa mijina bakin talaucin da zai sa ya daina cin amanata a titi - Addu'ar wata mata ga mijinta kenan

- Wata mata ta roki Allah wata bukata, wacce ta janyo kace-nace a shafukan sada zumunta

- Matar ta roki Allah ya sanyawa mijinta bakin talauci da ba zai iya zuwa ya ci amanarta da wata mace ba a titi

- Matar ta bayyana cewa maza na iya zuwa su kwanta da mace a titi ne kawai idan suka ji kudi a aljihunsu

Wata matar aure a Najeriya ta roki Allah wata mummunar bukata, hakan ya sanya mutane ke ta kace-nace a shafukan sada zumunta. Tambayar tata mai kama da abin dariya, wata kwararriyar mata a fannin zamantakewar aure, Joro olomofin, ita ce ta sanya a shafinta.

A wannan lokaci da muke ciki da ba a dauki cin amana a bakin komai ba, an gano cewa mazan da suka talauce basu da kudi suna shan wahala kafin su ci amanar matan su, domin kuwa yanzu harka ce ta komai sai da kudi, dole sai ka kashewa budurwa kudin kafin ta amince ta baka kanta.

A sanadiyyar hakane, wannan mata wacce ta bukaci Joro ta boye sunanta, ta yarda cewa idan har mijinta na cikin talauci, to babu hanyar da zai yi tunanin zuwa yaci amanarta da wata mace a titi, saboda maza da yawa suna bin matane idan suna da kudi a aljihunsu.

KU KARANTA: Rikicin siyasar Kaduna: El-Rufai na cikin tsaka mai wuya, yayin da jam'iyyar PDP ta nufi kotun daukaka kara

Ga abinda matar ta rubuto:

"Ya Allah ka kawowa mijina bakin talaucin da ba zai iya zuwa ya kwanta da wata mace a titi ba, kuma ka sanya mishi mutukar soyayyata a zuciyarsa, yaji tamkar zai hadiye ni. Ka mayar dani na zama mai juya shi a duk lokacin da nake so ta bangaren kudi. Idan ba shi da kudi matan titi baza su kula shi ba.

"Na yi wannan addu'ar a kaina da kuma dukkanin matan da suka karanta wannan sako nawa. Mu mata muna bukatar kwanciyar hankali, kuma hakan ita ce hanya guda daya kawai, ka dauke kudin mazajenmu hakanne zai sa su dawo su dinga yi mana biyayya. Duk wata mace da ta karanta wannan ina yi miki fata irin nawa," in ji matar.

Aure yanzu ya zama abin hakuri da juna, domin kowa yana neman dama ne da zai ci amanar dan uwanshi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel