Gawurtaccen mai garkuwa da mutane ya fadi ribar da suke samu daga muguwarsa sana'arsu

Gawurtaccen mai garkuwa da mutane ya fadi ribar da suke samu daga muguwarsa sana'arsu

Abubakar Umar, wani da ake zargi da garkuwa da mutane don karbar kudin fansa ya ce shi da tawagarsa sun samu zunzurutun kudi fiye da naira miliyan 2 na kudin fansa a cikin watanni shida da suka gabata.

Uwar, wanda 'yan sanda suka ce 'gawurtaccen mai garkuwa da mutane ne' ya ce suna gudanar da harkokinsu ne a jihohin Niger da Kebbi.

'Yan sandan sun bayyana cewa sun kama manyan motocci 28 dauke da buhunnan hatsi 1,972 da buhunnan wake 208 da za a kai mafakar masu garkuwa da mutane da 'yan bindiga da ke yankunnan Arewa maso gabas da Arewa maso yamma.

DUBA WANNAN: Hamshakan mata 5 da 'karan su ya kai tsaiko' a Najeriya

A cikin jawabin da ya yi a Abuja, Mai magana da yawun Rundunar 'Yan sanda, DCP Frank Mba ya ce tawagar 'yan sanda na Operation Puff Adder daga jihar Niger karkashin jagorancin DCP Kolo Yusuf ne sun kamo wani gaggararen dan bindiga.

"Wadanda aka kama sun hada da Abubakar Umar da akafi sani da Dogo Buba, Umar Mohammed, Usman Abubakar da Shehu Mohammed a Kainji, Mariga Bangi da Tsaragi a jihohin Niger da Kwara.

"Wadanda aka kama sun amsa cewa sun sace mutane da dama a jihohin Niger, Kebbi, Kwara da Osun kuma sun karbi kudaden fansa kafin suka saki wadanda suka sace."

Da ya ke bayani a kan Dogo, Mba ya ce: "Babban mai garkuwa da mutane ne da jami'an mu suka kama. Wanda ake zargin ya na da hannu cikin sace-sacen mutane cikin watanni shida kuma shi da kansa ya ce, sun samu kudi fiye da naira miliyan 200 a matsayin kudin fansa."

Mba ya kuma ce 'yan sanda sun bullo da sabuwar dabara ta dakile hanyoyin da bata garin ke amfani da ita domin samun abinci da makamai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel