Yanzu yanzu: Anyi harbe-harbe a Kaduna yayinda yan sanda suka tarwatsa yan Shi’a dake zanga-zanga

Yanzu yanzu: Anyi harbe-harbe a Kaduna yayinda yan sanda suka tarwatsa yan Shi’a dake zanga-zanga

An shiga halin dar-dar a rana Juma’a 31 ga watan Mayu a jihar Kaduna lokacin da jami’an yan sanda suka bude wutan harbi a sama domin tarwatsa mambobin kungiyar Shi’a, wadanda suka mamaye unguwanni domin zanga-zangar ci gaba da tsare shugabansu da gwamnati ke yi.

El-Zakzaky da uwargidarsa Hajiya Zeenat Ibrahim da wasu yan kungiyar na fuskantar tuhume-tuhume a babbar kotun jihar Kaduna da kotun Majistare bayan an kama su a watan Disamban 2015 biyo baya karawa da suka yi da sojoji a Zaria.

Dubban yan Shi’an, wadanda suka hada da mata da maza matasa, sun fara zanga-zangar jim kadan bayan sallar Juma’a a hanyar Kano inda suke ta ihun “Allahu Akbar, a saki shugabanmu”.

Yayinda suka mamaye hanyar Ahmadu Bello Way, babbar birnin Kaduna, sai kawai hukumomin tsaro suka tarwatsa su ta hanyar harba barkonon tsohuwa a sama, inda hakan ya tursasa masu zanga-zangar bin hanyoyi daban-daban.

Masu zanga-zangar sun haifar da fargaba a tsakanin mazauna yankin da kuma wadanda suka yi sallar Juma’a a yankin, domin hakan ya tursasa mutane yin gudu domin tsira da tsoron fadawa cikin rikicin.

Harbe-harben yan sanda ya kara haddasa tsoro a tsakanin mutane.

KU KARANTA KUMA: Wani babban jigon PDP da magoya bayansa sun sauya sheka zuwa APC

Yan sandan sun kakkabe hanyoyin Ahmadu Bello Way, Kano Road, Ibadan Street, Abeokuta Street da sauransu, yayina suka daidaita cunkoson hanya domin mutane su samu damarzirga-zirga cikin sauki sakamakon cunkoson da aka samu.

Sai dai babu tabbacin ko yan sanda sun kama masu zanga-zangar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel