Rayuka 36 sun salwanta, an yi garkuwa da mutane 27 a fadin Najeriya a makon daya

Rayuka 36 sun salwanta, an yi garkuwa da mutane 27 a fadin Najeriya a makon daya

Matsalar rashin wadataccen tsaro a Najeriya ta kai intaha cikin makon da ya gabata kadai inda dumbin al'umma suka rasa rayukan su yayin da wasu kuma suka afka cikin tarkon 'yan ta'adda masu garkuwa da mutane.

Shugaban kasa Buhari tare da shugabannin hukumomin tsaro na kasa

Shugaban kasa Buhari tare da shugabannin hukumomin tsaro na kasa
Source: Twitter

A yayin da kawowa yanzu kasar Najeriya ta gaza shawo kan kalubale na rashin tsaro da take ci gaba da fuskanta babu dare babu rana musamman a yankunan Arewacin kasar nan, ta'addancin masu garkuwa da mutane tare da neman kudin fansa ya zamto ruwan dare a kasar baki daya.

Shakka babu ta'addancin masu garkuwa da mutane ya zamto tamkar wata sana'a da zamto gama gari da masu aikata ta ke cin karen su babu babbaka kowace rana cikin dukkanin wani kwararo da sako na kasar nan.

Cikin makon da ya gabata kacal, 'yan Najeriya talatin da shida sun rasa rayukan su a hannun 'yan baranda yayin da mutane ashirin da bakwai suka afka cikin tarkon masu garkuwa da mutane jihohi daban daban da suka hadar da Kaduna, Ekiti, Edo da kuma Osun.

KARANTA KUMA: Sa'a 24 kafin rantsuwa, shugaban kasa Buhari ya gana da shugabannin tsaro na kasa a fadar Villa

Haka zalika wani mummunan harin 'yan kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram ya salwantar da rayuwar wani soji guda da jikkatar uku a jihar Borno. Kawo wa yanzu an kuma nemi sojoji shida an rasa kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel