Maganganu Aisha Buhari sun tabbatar da gaskiyar da muka dade muna fada - PDP

Maganganu Aisha Buhari sun tabbatar da gaskiyar da muka dade muna fada - PDP

Jam'iyyar PDP ta ce kalaman Aisha Buhari a kan shirin gwamnatin tarayya na bayar da tallafi (SIP) sun tabbatar da maganganun da suka dade suna yi a kan cewar gwamnatin APC na goyon bayan cin hanci da rashawa.

Da jam'iyyar ke mayar da martani a kan sukar da Aisha tayi a kan yadda ake sarrafa biliyan N500 da shugaban kasa ya ware da sunan shirin SIP, PDP ta bukaci hukumomin yaki da cin hanci su dauki matakan fara bincike a kan lamarin.

A ranar Asabar ne Aisha Buhari ta bayyana cewar shirin SIP ya gaza tabuka komai a arewacin Najeriya, tare da zargin Maryam Uwais, mai bawa shugaban kasa shawara a kan shirin bayar da tallafi, da rashin dacewa da mukamin da aka bata.

Uwargidan shugaban kasar ta bayyana hakan ne yayin wani taro da tayi da mata a fadar shugaban kasa, inda ta soki shirin da Maryam Uwais ke jagoranta.

Maganganu Aisha Buhari sun tabbatar da gaskiyar da muka dade muna fada - PDP

Kola Ologbondiyan
Source: UGC

Da take koka wa a kan yadda shirin na SIP ya gaza tabuka wani abun kirki a jihar Adamawa da ma yankin arewa baki daya, duk da irin makudan biliyoyin Naira da shugaban kasa ya amince da warewa shirin, Aisha ta ce ba zata yi magana mai tsawo ba don kar a ce ta fiye surutu, musamman ganin cewar sakataren gwamnatin tarayya ya fito ne daga jihar Adamawa.

A jawabin da Kola Ologbondiyan, sakataren yada labaran jam'iyyar PDP, ya fitar ya bukaci shugaban kasa Buhari ya yi magana a kan zargin da mai dakinsa tayi tare da daukan matakin da ya dace.

DUBA WANNAN: Duk lokacin da nayi magana sai a ce na cika surutu, ina sukar gwamnati - Aisha Buhari

"Babban abin haushin shine batun cewar an ware kudin ne domin walwalar talakawan da koda yaushe shugaban kasa ke ikirarin cewar su yake wakilta," a cewar sa.

Sannan ya cigaba da cewa; "tunda yanzu gaskiya ta fito daga bakin matar shugaban kasa, sai majalisa da sauran hukumomin yaki da cin hanci su fara gudanar da binciken yadda ake amfani da kudaden, musamman yadda ake kasafta su."

Ya kara da cewa matar shugaban kasan ta nuna cewar jam'iyyar PDP ba sharri ko kage take yiwa gwamnati ba tare da bayyana cewar tilas shugaba Buhari ya dauki alhakin dukkan wasu kudi da aka sace a gwamnatinsa a cikin shekaru hudu da suka gabata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel