Don sun ki yin PDP, gwamnatin jihar Sokoto ta ragewa da shugabannin makaranta 30 matsayi, an mayar da su aji

Don sun ki yin PDP, gwamnatin jihar Sokoto ta ragewa da shugabannin makaranta 30 matsayi, an mayar da su aji

Akalla shugabannin makarantan sakandare 30 a jihar Sokoto sun samu cibaya inda gwamnatin jihar ta mayar da su aji, matsayin da suka dade da wucewa sakamakon nuna bangarancin siyasa a zaben 2019.

Wadanda abun ya shafa sune shugaban kungiyar shugabannin makarantun sakandaren jihar ANCOPSS, Muhammad Musa, da sakataren kungiyar.

Daya daga cikin shugabannin ya bayyana cewa an mayar dasu aji ne sakamakon zargin nuna bangarancin siyasa.

Shugaban makaranta wanda aka sakaye sunansa, ya siffata wannan a matsayin cibaya da abin kunya saboda hakan zai kawo koma baya ga cigaban harkar ilimi a jihar.

Shugaban kungiyar ANCOPSS ya ce ba zai iya tabbatar da cewa anyi musu hakan saboda siyasa ba amma a matsayinsu na ma'aikatan gwamnati, sun rungumi kaddara.

KU KARANTA: Kalaman Obasanjo kan Boko Haram: Fadar Shugaban kasa ta mayar da martani

Kwamishanan ilimin makarantun firamre da sakandaren jihar, Farfesa Aisha madawaki, ta ce an nada kwamitoci kafin ragewa wadannan shugabanni matsayi.

Ta karyata rahoton cewa don siyasa ne aka yi hakan saboda kafin yanzu an ragewa wasu daga cikin matsayi zuwa mataimakan shugaban makaranta "amma tun da basu canza ba, an mayar da su aji."

A baya, jam'iyyar All Progressives Congress, shiyar jihar Sokoto ta kawo kuka kan yadda ake cin mutunci da muzgunawa mambobinta tun bayan kammala zaben gwamna a watan Maris.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel