Yadda kotu ta raba auren wani limami da ke kwanciya da 'ya'yan cikinsa guda uku

Yadda kotu ta raba auren wani limami da ke kwanciya da 'ya'yan cikinsa guda uku

- Kotu ta raba auren wasu ma'aurata wadanda suka shafe shekaru 41 suna tare

- Kotun ta raba auren ne bayan matar mutumin ta kai kararshi cewa bashi da aiki sai kwanciya da 'ya'yansu mata guda uku, kanwarta, kawayenta, da 'yan aiki

Jiya Alhamis ne wata kotu a Igando da ke jihar Legas, ta raba wasu ma'aurata wadanda suka kwashe shekaru 41 suna tare, ma'auratan masu suna Mrs Mabel Alli da mijinta Fasto Richard.

Alkalin kotun, Mista Adeniyi Koledoye, ya bayyana cewa, alamu sun nuna cewa ma'auratan sun gaji da zaman da suke, kuma sun kasa sulhunta kansu.

"Tun da ma'auratan sun amince da a raba auren, saboda haka wannan kotu ta kawo karshen zaman da suke.

"Daga yau kotu ta raba aure tsakanin Mabel Alli da Fasto Richard. Daga yau kun tashi daga matsayin mata da miji.

Yadda kotu ta raba auren wani limami da ke kwanciya da 'ya'yan cikinsa guda uku
Yadda kotu ta raba auren wani limami da ke kwanciya da 'ya'yan cikinsa guda uku
Asali: UGC

"Kowannen ku ya kama hanyar shi. Kotu na yi muku fatan alkhairi a rayuwarku ta gaba," in ji shi.

Mabel ta zo kotun ne, inda ta nemi kotun ta kawo karshen aurensu tsakanin ta da Richard, saboda ya yiwa 'ya'yansu da kanwarta ciki.

"Mijina yana kwanciya da 'ya'yanmu guda. Bayan ya yiwa kanwata ciki, ya dauki daya daga cikin 'ya'yanmu ya kai asibiti domin a zubar da cikin da ya yi mata.

"'Yar mu mai shekaru 19 ta kawo karar shi gurina, inda take fada mini kullum sai ya shiga dakinta ya kwanta da ita, nima da kaina na sha kama shi lokacin da ya ke kwanciya da su din.

"Kawayena da 'yan aiki ma basu tsira ba. Na sha kama shi dasu, mayen mata ne kawai," in ji matar.

Matar mai shekaru 63 ta ce mijinta yana da son kai sosai, domin yana so ya yi amfani da ita wurin tsafe-tsafen shi domin ya samu kudin da zai yi harkar siyasa.

KU KARANTA: An samu sabani tsakanin Naziru Sarkin Waka da Hadiza Gabon

Mabel ta ce mijin nata bai damu da 'ya'yan nasu guda hudu ba. Saboda haka ta roki kotu ta kawo karshen aurenta da shi.

Duk da Richard ya ki amincewa da zargin da matar tashi take yi mishi, shima ya yi maraba da raba auren, inda ya ce shima dama auren ya jima da fita daga ranshi.

Faston mai shekaru 66 ya karyata zargin matar na cewa yana kwanciya da kanwarta, kawayenta, masu aiki, da kuma 'ya'yansu, inda ya ce matar tashi ce ta kai 'yar tasu gurin zubda ciki.

A cewarsa, bai taba kai matarshi gurin boka ba kuma bai taba yi mata barazanar kasheta ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Asali: Legit.ng

Online view pixel