Majalisar dokokin Najeriya ta amince da wani kuduri akan Jakuna

Majalisar dokokin Najeriya ta amince da wani kuduri akan Jakuna

Majalisar dokokin Najeriya ta sanya hannu a wani sabon kuduri wanda zai bai wa Jakuna kariya daga safarar su da ake yi zuwa kasashen waje

Jiya ne majalisar dokokin Najeriya ta amince da wata doka wacce za ta haramta safarar Jakuna zuwa kasashen waje, dokar wacce aka gabatar a karo na biyu, majalisar ta ce yanzu ta na zaman jin ra'ayoyin al'umma ne akan dokar.

Majalisar dokokin Najeriya ta amince da wani kuduri akan Jakuna

Majalisar dokokin Najeriya ta amince da wani kuduri akan Jakuna
Source: Twitter

Wani dan majalisa mai wakiltar mazabar Illela da Gwadabawa na jihar Sokoto, Abdullahi Balarabe Salame, ya shaidawa manema labarai cewa daman lamarin ya dade yana damun al'ummar kasar nan, musamman ma a yankunan karkara wadanda suka fi amfani da jakuna a matsayin ababen hawa.

Jaki yana da amfani kwarai da gaske a karkara, ana amfani dashi wurin aikin gona, dakon kaya zuwa wurare daban-daban, debo ruwa, sannan akan yi amfani dashi wurin dauko mata marasa lafiya, musamman masu juna biyu a wasu lokutan.

KU KARANTA: Maganganu masu ratsa zuciya da Zainab Aliyu ta yi bayan dawowar ta gida Najeriya daga Saudiyya

Amma kuma a wannan lokacin Jakunan suna fuskantar barazana taa hanyar safarar su da ake yi zuwa kasashen ketare, musamman kasar Sin da suke amfani da fatun jakai wurin yin magunguna da sauran abubuwa na rayuwa.

Bayan haka kuma suna amfani da man shi wurin hada man shafawa wadanda mata ke amfani dashi, wanda aka tabbatar da cewa yana boye tsufan mace.

Majalisar ta na fatan da zarar an gabatar da dokar ta fara aiki, za a bayyana yadda za ayi amfaani da ita da kuma hukuncin da za a dauka ga wanda ya karya dokar.

Wannan shine karo na biyu da majalisar ta zauna akan maganar sanya doka akan safarar jakunan, sai dai zamanda ta yi a baya ba a cimma matsaya ba kamar wannan, da alamu wannan karon za a gabatar da kudurin ya zama doka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel