Zamfara: Shugaban karamar hukuma ya fadawa Minista irin barnar da aka yi

Zamfara: Shugaban karamar hukuma ya fadawa Minista irin barnar da aka yi

Mataimakin shugaban karamar hukumar Shinkafi da ke jihar Zamfara, Alhaji Sani Galadima, ya bayyana cewa an yi watsa-watsa da Garuruwa da kauyuka fiye da 98 a sanadiyyar haren-haren ‘yan bindiga.

Sani Galadima ya bayyana wannan ne a lokacin da Ministan harkokin cikin-gida, Janar Abdurraham Dambazzau mai ritaya ya kai ziyara zuwa jihar domin ganewa kan-sa irin barnar da ‘yan bindiga su ka yi a cikin ‘yan kwanakin nan.

Mataimakin shugaban karamar hukumar ya bayyanawa Ministan cewa zuba Sojoji da sauran jami’an tsaro da aka yi bai kawowa mutanen Yankin sauki ba. Galadima yace Jami’an tsaro ba su kawowa al’umma dauki a lokacin hari.

KU KARANTA: Boko Haram : An hallaka manyan Dakarun Sojin Najeriya

Zamfara: Shugaban karamar hukuma ya fadawa Minista irin barnar da aka yi
Aun bayyana irin ta’adin da aka yi a cikin Jihar Zamfara
Asali: Twitter

A jawabin na sa, Sani Galadima, ya nemi a kawo karshen wannan bala’i kafin ya kai ga cin sauran manyan Birane da Garuruwan Zamfara. A na sa bangaren, Abdurrahaman Dambazzau, yace gwamnati na yin bakin kokarin ta.

Laftana Janar Abdurrahaman Dambazzau, yace ta’adin ‘yan bindigan yana cikin manyan abubuwan da ke ci wa gwamnatin nan tuwo a kwarya, ya kuma ce tuni shugaba Buhari ya umarci jami’an tsaro su kawo karshen matsalar.

A cikin ‘yan kwanakin nan ne dai aka kashe mutane da-dama sannan kuma aka sace wasu, daga ciki har da Jami’an tsaro na-sa-kai 6 aka rasa. Jaridar Daily Trust ta bayyana mana wannan a jiya Litinin 13 ga Watan nan na Mayu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel